✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa: Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta cire kanta cikin alkalai

Shugabar Kotun Daukak Kara, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta cire kanta daga cikin alkalanr Kotun Musamman ta sauraron karar zaben Shugaban Kasa, inda ta ce…

Shugabar Kotun Daukak Kara, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta cire kanta daga cikin alkalanr Kotun Musamman ta sauraron karar zaben Shugaban Kasa, inda ta ce ta yi hakan ne saboda wasu dalilai nata.

Mai shari’a Bulkachuwa ta ajiye mukamin ne bayan kotun ta yi watsi da bukatar Jam’iyyar PDP da dan takararta na Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar na ta fita daga cikin masu sauraron karar domin a cewarsu suna tunanin ba za ta musu adalci ba saboda mijinta zababben sanata ne, kuma danta ya kasance dan takarar gwamna dukkansu a Jam’iyyar APC.

Da suke yanke hukuncin, alkalan Kotun ta Musamman mai mutum 5, duk sun yanke hukuncin cewa kawai kasancewa mahaifiya ko matar dan siyasa ba zai hana ta zama cikin masu sauraron karar ba, kasancewa iyalan nata ba sa cikin masu kara ko wadanda ake kara.

A yanzu sauran masu sha’arar hudu za su ci gaba da zama kafin a sanar da wanda zai maye gurbinta.