Da Dumi Dumi

Kotun ta rusa zaben dan majalisar APC

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta soke zaben dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ajaokuta a jJhar Kogi, Alhaji Mohammed Lawal. Alhaji Lawal  ya lashe zabe ne a karkashin Jam’iyyar APC, kuma ya samu nasara a karar da aka shigar a kotun kararrakin zabe a jihar.

Kotun ta umarci Hukumar INEC ta sake gudanar da sabon zabe a rumfuna 21 da ke mazabar. Dan takarar Jam’iyyar PDP, Aloysius Okino ne ya daukaka karar.

Hukuncin na zuwa ne kwanaki kadan bayan Kotun Koli ta tsige wani dan Majalisar Wakilai na APC mai wakiltar Lakwaja/Kogi, sannan ta bayyana Barista Shaba Isah Ibrahim na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Share