Aminiya

Kowa ya san sakaci ne ya sa aka yi gaba da ’yan matan Chibok – APC

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan

Jam’iyyar APC ta ba tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawarar cewa ya daina maida wa takawaransa tsohon Firayi Ministan Birtaniya Dabid Cameron martani, bayan da Cameron ya fito fili ya dora wa Jonathan laifi kan sace ’yan matan Chibok inda ya zargi Jonathan da hana a kubutar da su.                                                                                                                                                  Dokta Goodluck Jonathan ya kare kansa ne daga zargin sakacin inda ya ce wata kullaliya ce ta sa Cameron ya sa shi a gaba. Jam’iyyar APC ta fito fili ta ba Mista Cameroon gaskiya. Kakakin Jam’iyyar APC, Malam Lanre Issa-Onilu, ya ce kowa ya san sakacin da Jonathan ya saba ne ya haddasa  sace ’yan matan Chibok da aka yi sama da kwana 2000 da suka wuce.

Malam Lanre Issa-Onilu ya zargi gwamnatin Shugaba Jonathan da yi wa duniya karya kan yadda sha’anin sace ’yan makarantar na Chibok ya wakana. A ranar Asabar da ta gabata ce Issa-Onilu ya bayyana haka a Abuja inda ya ce abin da ya faru ya nuna aya game da irin rashin gaskiyar da aka rika tafkawa a lokacin da PDP take mulki.

ADVERTISEMENT

Jam’iyyar APC tana zargin gwamnatocin PDP da sace dukiyar kasa a shekara 16 da ta yi a kan mulkin kasar nan.

Jonathan ya dade yana musanta zargin sakacinsa a sace ’yan matan na Chibok lokacin mulkinsa.

ADVERTISEMENT