✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Koyar da almajirai sana’a za ta hana barace-barace’

An shawarci malaman makarantun allo su rika barin almajiransu suna koyon sana’o’i don rufa wa kansu asiri da kuma kare su daga shiga wasu ayyuka…

An shawarci malaman makarantun allo su rika barin almajiransu suna koyon sana’o’i don rufa wa kansu asiri da kuma kare su daga shiga wasu ayyuka da ba su dace ba da wadansu ke son fakewa da su don hana harkar almajirci a kasar nan.

Malam Adamu Shehu wani malamin makarantar allo da ke cikin garin Kafanchan ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya kan hanyoyin magance cece-ku-cen da ake yi kan illolin  bara da yunkurin hana almajirci da wadansu ke ta kiraye-kiraye a kai, inda ya ce idan malamai suka bari almajiransu suka koyi sana’a, kamar yadda nasa suke yi, ba sai an ce kada a fita barace-barace ba.

Ya ce almajiransa ba sa bara saboda hatta kanana daga ciki suna da sana’ar da suke gudanarwa idan sun tashi karatu ko kuma ranakun da ba makaranta.

“A cikinsu akwai masu iyayen gida da sukan je su gudanar musu da aikatau a biya su, yayin da wadansu kuma ke fita sana’a kamar yankan farce da wankin takalmi ko wanki da guga inda suke samun abin da suke biya wa kansu bukatu da shi,” inji shi

Malamin ya ce shi ma yakan hada koyarwar da wasu ayyuka da suka hada da dinki da wankin hula, don haka ya san muhimmancin koyon sana’a ga mutum musamman ga wanda ba ya da mai taimaka masa.

Ya yi kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni su da bada himma wajen tallafa wa malamai da almajirai ta hanyoyin da suka dace wanda malaman za su ji dadi kuma daliban su tashi da abin dogaro da kai.

Wani almajiri da Aminiya ta samu yana gyara da wankin wasu takalma, ya ce duk ranakun da babu makaranta da kuma lokutan da aka tashi karatu maimakon su tafi bara, sai kowa ya fita sana’arsa.

“Ni ina aikin dinkin takalma ne kuma a duk ranar da ba makaranta idan na fita nakan samu Naira dari biyar wanda nake adana wasu sannan nake yin amfani da wasu don rufa wa kaina asiri kuma ina samun natsuwa lokacin karatu saboda ba wani abu da nake tunani da zai dauke min hankali domin ina da sana’a,” inji shi.

Abdullahi Ali, dan kimanin shekara 12 da ya ce yana cikin Izifi na biyu ne, ya ce ya rungumi sana’ar ce saboda ya ga sauran ’yan uwansa da ke makarantar na yin sana’a, sannan ya ce idan gwamnati da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni za su tallafa musu wajen koya musu sana’o’i tare da karfafa su da jari, to za a rage kashi mai yawa na barace-barace ba sai an jingina musu munanan ayyuka ba.