Da Dumi Dumi

‘Ku bar ni in fita!’ Gawa ya fada wa  masu binne shi a kabari

Wadanda suka halarci binne Shay Bradley
Wadanda suka halarci binne Shay Bradley

Wadansu masu binne gawa a makabarta sun firgita lokacin da suka ji murya daga cikin kabarin kamar sautin lasifika daga cikin kasa. Daya daga cikin ’yar uwan mamacin ta yi matukar razana, daga bisani sai ta tuna kalaman barkwanci da ya fada na karshe kafin rasuwarsa, wadanda ya yi a matsayin ban-kwana.

Masu binne gawar mamacin a makabartar sun bar makabartar cikin tsoro sakamakon  muryar da suka ji daga cikin kabarin, yana cewa, “Ku barni in fita, cikin nan akwai duhu.”  Mamacin suna Shay Bradley da ke cikin akwatin gawa an sanya shi a kabarin da aka haka a garin Kilmanagh, da ke Karamar Hukumar Kilkenny a Jihar Leinster, ta kasar Ireland a ranar 12 ga watan Oktoban nan.

A cikin sakon da aka nada na muryar, na ci gaba da cewa, “A ina nake yanzu? Wannan muryar malam ce? Ni ne Shay a cikin makara.”

Sai ya fara waka yana cewa: “Halo, halo, halo na kira ne in yi muku ban-kwana.” Sai ya fara dariyar karshe da ya yi lokacin lda ake yaye su a matsayin tsofaffin sojojin Ireland. Ya rasu ne yana da shekara 62, hakan ya sa wadanda suke wurin suka fara zubar da hawaye.

’Yar Mista Shay, mai suna Andrea Bradley, ta ce mahaifinta ya dade yana rashin lafiya inda ya kai shekara uku yana jinya kafin ya rasu a ranar 8 ga Oktoban bana. Ya hada sakon barkwancinsa ne a bara. Kamar yadda Andrea ta bayyana wa kafar labarai ta Sky News. Ta kara da cewa, mahaifinta mutum ne mai son harkokin rayuwa.

ADVERTISEMENT

Andrea, ta ce “Dan uwana mai suna Jonathan ya girma ne a gaban mahaifina har zuwa shekararsa ta karshe kafin ya rasu, wadansu kadan daga cikin ’ya’ya da jikokinsa ba su san wadansu daga cikin harkokinsa ba.” Wadansu daga cikin jama’ar da suka halarci binne Shay, sun dade suna mamakin ta yadda suka ji murya daga cikin kabarin Shay ta sautin lasifika.

“Amma duk da haka, sai muka ce muna cikin jimamin rasuwar Shay, lokaci ne da za a yi bikin rasuwarsa yanzu. An dauki lokaci ana tafka muhawara a kan wannan abu ya faru shafukan sada zumunta na zamani.” Kuma bidiyon binne Shay, ya dauki hankalin jama’a da dama musamman a shafukan Facebook.

Rundunar Sojojin Ireland ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan tsohon sojan kasar Shay Bradley. Kuma ta yi masa addu’a a cikin wasu sakonni da dama da aka yi ta tura wa iyalansa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya