✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ku kai ‘ya’yanku makaranta ko ku dandana kudarku’

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta gargadi iyaye da su tura ‘ya’yansu makaranta ko kuma su dandana kodarsu. Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta jihar…

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta gargadi iyaye da su tura ‘ya’yansu makaranta ko kuma su dandana kodarsu.

Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Misis Phoebe Yayi ce ta bayyana hakan, tana mai cewa ko wanne yaro na da hakkin samun karatu kyauta a matakin firamare da sakandare kuma hakkin gwamnati ne ta samar da hakan.

Ta kara da cewa wannan ne ya sa gwamnati ta sanar da shirinta na bayar da ilimin firamare da sakandare kyauta a duk fadin jihar.

“Dokar ‘yancin yara ta 2018 ta bayyana cewa duk iyaye ko wakilan yaron da suka ki kaisu makaranta to sun aikata laifi.

Kuma za a iya hukunta su ta hanyar, gargadi, aikin gwala-gwala, tara ko kuma dauri a gidan kaso,” kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

A don haka ta yi gargadin cewa kai yara makaranta wajibi ne ba wai zabi ba.

Arewacin Najeriya na kan gaba wurin yawon yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan, kuma gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu na cewa suna kokarin shawo kan lamarin.

Sai dai har yanzu wasu masu lura da al’amura na cewa babu wani cikakken cigaba da aka samu.