Da Dumi Dumi

Ku kawar da bara-gurbin da ke cikinku – Kwamandan Soji

Kwamandan Shirin Tabbatar da Zaman Lafiya na ‘Operation Sabe Haben’ da ke kula da harkar tsaro a jihohin Filato da Bauchi da kananan hukumomi biyar da ke Kudancin Kaduna, Manjo Janar Augustine Chukwudi Agundu ya yi kira ga makiyaya da manoma su tsabtace kabilunsu daga batagarin da ke cikinsu wadanda suke haddasa fitina a daidai lokacin da kasar nan ke bukatar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Janar Augustine Agundu ya yi wannan kira ne yayin gudanar da wani taro da suka shirya tare da masu ruwa-da-tsaki da suka hada da shugannin addinin Musulunci da na Kirista da sarakunan gargajiya da kungiyoyin manoma da na makiyaya da suka fito daga kananan hukumomi biyar da aka fi samun hatsaniya a Kudancin Kaduna.

Janar Agundu ya ce babu wata kabila da za ta tsarkake kanta don haka su guji nuna wa juna yatsa don tunkarar matsalar daga tushe.

“Babu ranar da za mu samu zaman lafiya idan ba mu daina kallon laifi a jikin wata kabila ba. Kowace kabila akwai bara-gurbi a cikinta, don haka idan kowa ya ci gaba da boye mai laifi bayan ya san su don ci gaba da dora wa wata kabila laifi, to kada ku zargi kowa da rashin samar muku da zaman lafiya,” inji shi.

Sannan ya zargi manya da tsofaffin ma’aikatan yankin da ba sa zaune a yankin a matsayin masu rura wutar rikicin, yayin da su da iyalansu ke can a manyan birane suna hutawa.

ADVERTISEMENT

Da yake nasa jawabi, Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmad El-Rufa’i wanda Kwamishinan Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan ya wakilta, ya nanata matsayin Gwamnatin Jihar Kaduna kan daukar kwararan matakai ga duk  masu neman tayar da fitina a fadin jihar, tare da yin kira ga jama’a su rika gaggauta sanar da hukuma duk wani al’amari da ya taso ko yake shirin tasowa a yankinsu da ka iya haifar da tashin hankali.

Mista Aruwan ya ce, “Idan har ba mu kalli laifi a matsayin laifi ba, sai mun cusa maganar addini ko kabila a ciki, to babu ranar da rigima za ta kare.”

A karshe ya yi kira ga kowane bangare ya daina daukar doka a hannu duk lokacin da wani abu ya faru, maimakon haka, su rika barin hukuma ta gudanar da bincike da kuma hukunta wanda doka ta kama da laifi.

Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na makarantar Sakandaren GSS da ke Kafanchan, ya samu halartar wakilai daga kungiyoyin manoma da na makiyaya da na matasa da sarakunan gargajiya da malaman addini.

 

 

Share