Kulob din Ahmed Musa ya zama zakara a Saudiyya

Ahmed Musa

A ranar Lahadin da ta wuce  kulob din Ahmed Musa Al Nassr ya lashe Kofin Super na Saudiyya bayan ya lallasa kulob din Al Taawon a bugun fanariti.

An tashi wasan ne da ci 1-1 inda aka yi bugun finareti inda kulob din Al Nassr ya zura kwallo biyar a raga yayin da Al-Taawon ya zura kwallo hudu ya barar da kwallo daya.

Wannan shi ne kofi na biyu da Ahmed Musa ya lashe a kulob din Al Nassr bayan da ya koma Saudiyya daga kulob din Leicester City na Ingila kimanin shekara biyu da suka gabata.

Sai dai ana gab da tashi wasan ne aka canja Ahmed Musa da Abdulfattah Mohammed Adam.  Sannan dan kwallon Al Nassr Abderrazak Hamdallah ne ya zama sanadin cin da kulob din Al Taawon ya yi musu a daidai minti na 43.

ADVERTISEMENT
Share