Da Dumi Dumi

Kundin  Mulkin Masarautar Kano (2)

Ƙofar Gidan Sarkin Kano; Gidan Rumfa

A wannan mako za ci gaba da bayani  ne kan Masarautar Kano inda muke kawo karashen  abin da ke kunshe a cikin littafin Tsarin Mulkin Masarautar Kano da Shehi Magili ya samar a zamanin daya daga cikin sarakunan Habe, wato Sarki Muhammadu Rumfa:

 

Babi na Huɗu

Wannan babi ne da ya yi magana game da zaman jiran ko-ta-kwana a lokacin da ake zaune a gida ko a halin tafiya a yayin da yanayi ya canja daga aminci zuwa tsoron kawo hari daga abokan gaba da kuma irin matakan da suka kamata Sarki ya ɗauka. Malam ya ce:

Lazimtar taka-tsantsan a halin zaman gida ko kuma na tafiya ta hanyar bayyanar da ƙarfi da kuma juriya (juriya a nan na nufin Sarki ya jure wa dukkan irin firgici, razani da tsoron da yake ransa, ya danne shi kada ya sake ya bayyana a fili, mabiyansa su gane. Hakan zai karya musu gaba) a yayin canjawar yanayi zuwa na tsoro.

ADVERTISEMENT

Ya zama mai bayyana gudun-duniya a cikin abin da ya shafi matarsa da ɗansa saboda kada su hana shi aikata adalci “Lallai ne daga matanku da ’ya’yanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu.” (Alƙur’ani, 64:14).

Ya zama mai bayyana kwaɗayinsa wajen rashin ɗaukar ɓangare da kuma daidaito. Sannan ya zama mai son fita zuwa jihadi. Ya zama mai ƙin zama a cikin gida. Wannan zai ɗaukaka kimarsa a idon abokan gaba.

Zaman Sarki a cikin gidansa ga barin jama’arsa, shi ne tushen kowace fitina da kuma ɓarna. Shi mulki da takobi ake yin sa ba da sanyin jiki ba. Abin nufi, ba zai yiwu da faɗin cewa da sannu zan kai musu hari, da sannu zan aikata ba. Anya kuwa zai yiwu a kawar da tsoro a cikin firgici? Tabbas duk wanda ya tsoratar da kai, to kada ka miƙa masa wuya sai ka razana shi kuma ba tare da ka yaƙe shi ba ko ka nemi sasantawa da shi ba. “Kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zuwa ga sulhu alhali kuwa ku ne mafiya ɗaukaka, kuma Allah Yana tare da ku.” (Alƙur’ani, 47:35).

Dole ya zama mai taka-tsantsan a cikin abincinsa da abin shansa da makwancinsa. Kada ya jiɓintar da kowa sai makusanta kuma masoyansa.

Kada ya zauna a majalisa ba tare da jaruman mayaƙan ƙasa da kuma mahaya dawaki ba. Kuma su zama amintattu sannan kuma jarumai. Lokacin zaman ɗar-ɗar ba ɗaya yake da lokacin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

Ya zama mai ɓoye sirrinsa. Kada ya riƙa yarda da zantukan annamimai ko da sun haura saba’in. Su kuwa masu zato (abokan gaba), kada ya yaudaru da bayyanar ’yan aikensu, kyautar girmamawa tana amintar da su. Gwarazan cikinsu kuma a ba su babbar kyauta. “Kuma lallai ni, mai aikawa ce zuwa gare su da kyauta, sa’an nan mai dubawa ce da me manzannin za su komo.” (Alƙur’ani, 27:35).

A cikin abin da ya shafi garuruwan da ke kusa da maƙiya, ya rushe dukkan garuruwan da ba zai yiwu amintattunsa su zauna a ciki ba. Saboda kada (garuruwan) su tanadar masa maƙiya. Ya nisanci igiya saboda gudun cizon maciji. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Babi na Biyar

Babi ne da ya yi magana a kan wasu al’amuran rayuwa masu rikitarwa waɗanda suka zama dole Sarki ya warware su ta cikin hikima, bisa amana da kuma adalci. Malam ya ce:

Babi na biyar, cikin abubuwan da suka zama dole a warware su bisa adalci da amana daga cikin abubuwan da suke shige wa talakawansa duhu kamar lamarin waɗanda aka tsare dukiyarsu. Marayan da aka hana shi sarrafa dukiyarsa to mai kula da shi ne zai ɗauki ɗawainiyar rayuwarsa.

Haka nan a saka tsantseni da lura wajen warware al’amuran da suka shafi ɓoyayye (mutumin da ya yi tafiya sannan ya ɗauki dogon lokaci babu labari) da gadon matattu da alamuran dukiyar al’umma da kuma albashin ma’aikata. Kada a saka cutarwa da kwaɗayi a ciki. Kamar abin da ya shafi albashin ma’aikatan kuɗi na daga abin da yake ƙaruwa a gare su na kuɗi.

Duk wanda yankewa ta bayyana a gare shi (wato duk wanda ya yanke wa wani kuɗi; wanda aka iya zama albashi ko waninsa, kuma aka gane), to, a tsawatar masa. Wanda kuma ya yi zalunci a cire shi. Wanda kuma ake yin ƙorafi a kansa a canja shi idan za a samu wanda zai canje shi. idan kuma ba haka ba, to Sarki ya rasa amintattu.

Duk wanda kuɗi (dukiyarsa da kadarorinsa) suka ƙaru a kan abin da ya dace a biya shi (ya mallaka), to a karɓe (karin) a saka shi a cikin gyaran al’amuran Musulmi. Idan kuma aka yi kokwanto a kai, to a rantsar da shi (wato idan ya ce nasa ne sai a saka shi ya rantse a kan haka). Ya (Sarki) kasance a gare su (talakawan) kamar mai kiwon dabbobi a tsakanin mafarautan zakuna (wato zakunan da suke farautar abinci). Dukkan ɓarna tana tare da gurɓataccen albashi.

Aikin ma’aikatanka aikinka ne, idan ya kyautatu, ladan naku ne baki ɗaya, idan ya munana, horon yana kanku.

Game da masu burin aikata ɓarna, haƙiƙa buri yana tabbata da samuwar alamomi. Babu makawa wajen warware shi idan aka tabbatar da shi. Idan kuma ba haka ba, to sai a hukunta shi bisa dacewa gwargwadon kusancinsa da nisansa. Sannan kuma a toshe kafar aikata laifin.

Game da abin da ya shafi al’amuran abokan gaba kuwa, to babu makawa wajen warware shi ta hanyar leƙen asirin amintattu. Haƙiƙa jahilci makanta ce. Mutum ɗaya mai ido zai iya rinjayar makafi dubu. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne ya wofintar da talakawansa. Zargin masu zargi da yabon masu yabo, dole a warware su ta hanyar amintattu.

Babi na Shida

Abubuwan da suka zamar masa dole ta fuskacin adalci da kuma kyautatawa. Abin da ake nufi da adalci shi ne a bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa. Duk ɗaya ne zamowar haƙƙin nasa na ƙashin kansa da kuma na talakansa. Duk wanda baya bai wa talakawansa haƙƙin da ya shafe su to wannan ba adali ba ne.

Ita kuwa kyautatawa, ita ce ya fifita da kansa. Abin nufi shi ne ya ƙara wa duk wanda ya yi nufin ya kyautatawa; ƙari daga cikin abin yake shi ne haƙƙinsa, amma ba da rabon waninsa ba. Duk wanda ya kasance yana kyautata wa mutane ta hanyar ba su fiye da abin da suka cancanta daga cikin dukiyar da dukkan jama’a suka yi tarayya a cikinta ba tare da yardarsu ba, to bai zama mai kyautatawa ba, maimakon haka ma shi azzalumi ne. Saboda abin da ya yi kyautatawar da shi bai keɓanta da shi ba a shari’ance. Ka fahimci wannan lamarin, kada ka yi burinsa.

Adalci ne daidaita tsakanin mutane masu rigima a cikin dukkan lamuransu. Kuma kada ya karɓi shaida sai ga wanda ya kasance adali kuma yardajje; wanda babu tuhuma a kansa. Idan kuma adalcin ya wuyata, to ya lura da kwatankwacinsa ta fuskacin gaskiya tare da bayyanarta wato sanuwa a kan gaskiya. Kada ya wadatu da guda biyu, kuma ya zama akwai siyasa da lura a cikin lamarin. Sannan dole ya yi wa wanda ake ƙara bayanin dalilan da suka saka aka yi ƙararsa, sannan ya kafa masa hujja idan yana nufin hukunta shi; dole ya yi masa cikakkiyar warwara game da dalilan da suka tabbatar da hukuncin a kansa. Sannan ya kafa masa hujja da cewa: “Ko kana da sauran hujja?” Idan ya ce akwai, sai ya sake yi masa warwara. Idan kuma ya ce babu, sai a hukunta shi. Kuma hukuncin ya zamo bayan an tuntuɓi malamai. Baya halatta ya hukunta ko ma mene ne sai bisa abin da ya bayyana a mazahabar limaminsa. Tabbas hukunci da wanin abin da aka saba da shi zalunci ne, sannan taɓewa ce, kuma dole a warware wannan hukunci ta kowane hali.

Ikirarin manyan laifuffuka yana keɓantuwa da nau’o’in siyasa. Manyan laifuffuka kuwa su ne irin su sata da kisan kai. Duk wanda aka ce ya yi sata ba tare da hujja ba, to ba zai kuɓuta daga ɗayan abubuwa uku ba:

Na Farko: Idan ya kasance ya nesanta daga abin da aka dangata shi da shi, to a yi watsi da maganar sannan a ladabtar da wanda ya faɗi maganar idan wanda aka faɗi maganar a kansa ya kasance mutumin kirki ne.

Na Biyu: Idan ya kasance ya kusanci abin da aka danganta shi da shi, to dole a kama shi a tsare, a hukunta shi da bulala gwargwadon laifinsa tare da jin tsoron Allah a cikin lamarin. Wasu lokutan zai iya kuɓuta ko laifin ya tabbata a kansa, to sai ya yi rantsuwa kamar yadda aka saba. Saboda sanuwa da ya yi da kuma yawan maimaituwar maganar a kansa, hujja ce a wurin wanda ya faɗi maganar a bisa abin da aka saba da shi. Duk wanda aka yawaita yi masa horo har ya sanu da wannan, to a tsare shi har sai tubarsa ta bayyana ko kuma a aika shi ƙabari.

Na Uku: Idan ya kasance miskili ne shi, sai a tsare shi har sai alƙali ya fahimci irin halinsa, sannan a yi masa hukuncin da ya dace. Idan kuma ba haka ba, to a sake shi. Hakan zai zama siyasa tare kuma da horo da bincike; gwargwadon yadda saka ido da shaida za su iya hukunta shi. Dukkan waɗannan a yi su bisa tsoron Allah ba bisa son zuciya ba. Mutane ba su taru sun zama ɗaya ba.

Duk wanda aka ce ya yi kisan kai, to dole a kama shi a tsare a matakin farko. Idan kuma laifin ya tabbata a kansa sai a hukunta shi. idan kuma ba haka ba, to sai a lura da duk wanda yake cuɗanya da su ta fuskacin nisa da kuma kusanci. Idan ya kusanta (da laifin), to sai a tsawaita ɗaurin. Idan kuma ya nesanta sai a gaggauta sakinsa.

Dole ne babban sarki ya riƙa zama (a majalisarsa) a kowace rana domin dukkan talakawansa su riƙa samun zuwa gare shi. Ma’aikatansa da sauran masu riƙe da sarautu ba su isar masa ba. Saboda ƙorafin waɗanda yake mulka zai iya kasancewa a kansu ne. Saboda haka dole ya gargaɗe su. Idan kuma ba haka ba, to ya zama kamar kwando ga kayan cikinsa ko kuma mariƙin ƙahon saniyar tatsa. Haƙiƙa an cire nagartattun ma’aikata masu wakilci saboda koke. Wannan kuma shi ya fi kusa da jin tsoron Allah. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga littafin: Kano ta Dabo Cigari na Wazirin Kano A. A. (1978), wallafar Northern Nigerian Publishing Company Limited. Zariya, Jihar Kaduna. Da kuma shafin Intanet.

Mun kammala

 

 

Share