✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta bukaci masu cutar laka su daina fid da tsammani

Kungiya Tabbatar da Ci gaban Rayuwar Masu Cutar Laka  (RHOWI) ta yi kira ga masu fama da wannan lalura da kada halin da suke ciki…

Kungiya Tabbatar da Ci gaban Rayuwar Masu Cutar Laka  (RHOWI) ta yi kira ga masu fama da wannan lalura da kada halin da suke ciki ya sa su karya da rayuwa kasancewar masu fama da wannan lalura za su iya ci gaba da karatu da samun guraben ayyuka a ma’aikatun gwamnati.

Shugabar Kungiyar RHOWI, Hajiya Amina B. M. Abdu ce ta yi wannan kira lokacin da shugabannin kungiyar suka ziyarci masu fama da lalurar laka da ke kwance a Asibitin Kashi na Kasa da ke Dala a  Kano don taya su murnar zagayowar Ranar Nakasassu ta Duniya.

Hajiya Amina ta ce duk da cewa ta shafe shekara 32 a kan kujera, amma hakan bai hana ta ci gaba da karatu ba inda a yanzu ta kai matsayin malama a daya daga cikin manyan makarantun da ke kasar nan.

“Duk da mun san cewa wanda ya kamu da wannan cuta ba zai dawo kamar da ba, to amma hakan ba ya nufin mutum ba zai ci gaba da harkokin rayuwarsa ba. Mutum zai iya yin karatu har ya yi aiki kamar yadda  muka yi. Mutum zai yi aure har ya haihu da sauransu,” inji ta.

Hajiya Amina ta yi kira ga masu lalurar su dauki hakan a matsayin kaddara tare da kokarin kula da kansu, don guje wa aukuwar wasu cututtukan sakamakon rashin kulawar da ba su yi, “Ita wannan cuta tana haifar da wasu cututtuka ga mai lalurar sakamakon rashin kulawa, misali akan samu matsalar koda da shigar kwayoyin cuta a mafitsara sakamakon rashin shan isasshen ruwa da kuma yiwuwar samun miki sakamakon rashin zagayawar jini a jikin mai lalurar. Don haka akwai bukatar kula da kai ta hanyar shan ruwa sosai da kuma

duba jiki akalla sau biyu a rana,” inji ta.

Hajiya Amina ta yi kira ga gwamnati ta samar da cibiyar kula da masu lalurar laka, kasancewar a cewarta duk fadin kasar nan babu inda ake da irin wannan cibiya.

A lokacin ziyarar, Kungiyar RHOWI ta rarraba wa marasa lafiya kayyayakin da sabulu da turaren daki da hoda da madubi da safar hannu da jakar tara fitsari da sauran kayyayaki don saukaka musu rayuwar asibiti.

A jawabinsa Shugaban Asibitin Kashi na Dala, yaba wa kungiyar ya yi bisa tallafin da ta bayar ga marasa lafiya da ke asibitin kasancewar abu ne da zai zama na kafafa gwiwar masu wannan lalura game da sha’anin da ya shafi ci gaban rayuwarsu.