✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta horar da malaman Ingilishi a Dambatta

Kungiyar Rayawa da Habaka Harshen Ingilshi da Adabi ta Karamar Hukumar Dambatta a Jihar Kano ta gabatar da taron kara wa juna sani ga malaman…

Kungiyar Rayawa da Habaka Harshen Ingilshi da Adabi ta Karamar Hukumar Dambatta a Jihar Kano ta gabatar da taron kara wa juna sani ga malaman makarantun firamre da sakandare masu koyar da harshen Ingilishi a karamar hukumar.

Taron mai taken “Sababbin Dabarun Koyo da Koyar da Harshen Ingilishi Cikin Nishadi” ya samu halartar malamai sama da 200.

Bako mai jawabi kuma Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke  Kano, Farfesa Mustapha Ahmad Isah ya yi bayani ne game da koyon Nahawun Ingilishi da dabarun da malaman za su bi wajen koyar da shi. “Abu ne mai sauki matuka a matsayinku na malamai za ku zage dantse tare da mayar da hankali wajen koyonsa,” inji shi.

Tun farko a jawabin Sakataren Kungiyar Malam Sa’idu Mustapha Buhari ya tabo tarihin kafuwar kungiyar  wanda ya ce an kafa ta ce musamman saboda bunkasa harshen Ingilishi da yanzu yake ba dalibai matsala wajen furta shi da kuma rubuta shi.

A cewarsa, kungiyar tana gabatar da shirye-shirye da dama kamar shirya bita da tarurrukan kara wa juna sani da sanya gasa da muhawara a tsakanin dalibai da sauran abubuwa don ci gaban ilimin dalibai.

Tsohon Mataimakin Daraktan Ilimi Shiyyar Dambatta ya yaba wa kungiyar kan shirya taron da ta yi wanda a cewarsa shi ne irinsa na farko a karamar hukumar kuma ya yi kiran a ci gaba da gudanar da shi lokaci bayan lokaci.

Musbahu Ahmad, malami ne a Makarantar Firamaren Barde da Maryam Abdulhamid daga Makarantar Jamila Islamiyya sun nuna jin dadinsu kan bitar da aka yi musu domin a cewarsu sun karu kwarai da gaske.