✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta kaddamar da gidauniyar tallafin ilmi

Gidauniyar bayar da tallafin ilmi da kiwon lafiya ga marasa galihu da kungiyar ‘Garin Na-Garke-Group’ ta kaddamar cikin makon jiya a Ibadan, ta ce kananan…

Gidauniyar bayar da tallafin ilmi da kiwon lafiya ga marasa galihu da kungiyar ‘Garin Na-Garke-Group’ ta kaddamar cikin makon jiya a Ibadan, ta ce kananan yara da ake kora daga makarantu a dalilin kasa biyan kudin makaranta da gajiyayyun mutane masu lalurar asibiti su ne za su amfana da tallafin gidauniyar.

“Za a bayar da tallafin kudi da bai gaza Naira dubu 20 ba, ga wanda aka tabbatar da mabukaci ne kuma mun nada kwamitin amintattun mutane 11 da zai lura da harkokin gidauniyar tare da yiwuwar kara yawan kudin tallafin nan gaba da zai kai ga daukar nauyin kudin tallafin karatu na mabukatan.”

Jagoran wannan kungiya Mataimakin Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa (NPA) Alhaji Ali Nakamba shi ne ya fadi hakan cikin zantawarsa da Aminiya. Jim kadan bayan kammala taron musayar ra’ayi da manbobin kungiyar suka yi tare da kaddamar da gidauniyar a zauren taro na Premier Hotel da ke Ibadan. Ya ce, “Mun radawa kungiyar sunan ‘Garin Na-Garke-Group’ ne domin lura da irin rawar da wannan mutumi marigayi Muhammadu Na-Garke ya taka shekaru kusan 100 da suka wuce a lokacin da masarautar Ibadan a karkashin Sarkin Ibadan Baale Irefin, da amincewar (DO) ta mikawa Nagarke wani daji a kusa da tsaunin Mokola a matsayin Sabon gari a shekarar 1914 da ya zama unguwar Sabo mazaunin Hausawa a yanzu.”

Ya ce, “Manbobin kungiyar Hausawa ne zalla da iyaye da kakanni suka Haife mu cikin Unguwar ta Sabo a birnin Ibadan hedkwatar Jihar Oyo da yanzu haka Allah Ya daukaka matsayinmu zuwa manyan mukaman gwamnati da attajiran ’yan kasuwa da ‘yan siyasa da muka hadu muka kafa kungiyar da kaddamar da gidauniyar domin taimakon ’yan uwa marasa galihu da ke zaune a wannan unguwa.”

‘Kaddamar da gidauniyar ya biyo bayan lura da tabarbarewar ilimin zamani musamman ga ’ya’yan marasa galihu a cikin wannan unguwa da tayi fice a garin Ibadan cibiyar ilmin boko a Najeriya. Irin wadannan yara sukan zama abun tausayi a karshen rayuwa. Kuma akwai mutanen da suka tagayyara a dalilin kamuwa da wata cuta da suke kasa biyan kudin Asibiti da gidauniyar za ta rinka tallafa masu bayan an tantancesu.”

Alhaji Ali Nakamba, ya ce “Kungiyar ta sake dawo da hawan daushe da hawan gaisuwa ga Sarkin gari Olubadan da hawan gidan gwamnati domin gaisuwar Gwamna da aka saba yi a baya domin gujewa bacewar al’adunmu a cikin mutanenmu da ke zaune a wannan yanki. Fafutukar neman ’yanci daga mahukunta yana daga cikin muhimman abubuwan da kungiyar Garin Na-Garke-Group tasa a gaba da za mubi kyawawan hanyoyi wajen isar da kukanmu. Daya daga cikin irin wannan koke shi ne rashin samun manya da kananan mukamai daga bangaren Gwamnatin Jihar Oyo duk da dadewarmu zaune a wannan gari na Ibadan alhali wasu Gwamnatocin Jihohin Arewa suna bayar da irin wannan mukamai ga kabilun Yarbawa. Za mu iya cimma wannan buri ne idan muka hada kai da kishin ’yan uwa ba kamar yadda muke zaune kara zube da ’yan siyasa a wannan yanki suke amfani da kuri’unmu a lokutan zabe da mantawa damu bayan sun yi nasara ba,” in ji shi.

Taron shi ne irinsa na farko da haifaffun Hausawan Ibadan suka yi a inda suka yi musayar ra’ayi da zai kai ga cimma burinsu. Babban bako Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru, ne ya jagoranci Sarakunan Hausawa dukkan su haifaffun Sabo ne da suka halarci wajen taron. Manyan malaman addinin musulunci ’yan Sabo sun yi addu’o’in rokon Allah (SWT) Ya sanya albarka ga wannan kungiya. Su kuwa ’yan boko kamar Farfesa Yusuf Dankofa na Jami’ar ABU Zariya da Farfesa Kyauta Ibrahim na Jami’ar BUK Kano da Dakta Zakari Salisu Hambali na Federal Polytechnic Auchi, dukkan su haifaffun Sabo Ibadan sun gabatar da lakcoci da shawarwari a kan tarihin Hausawan Ibadan da zamantakewa tsakaninsu da Yarbawa da irin rawar da suke takawa wajen bayar da gudunmawar bunkasar tattalin arzikin Ibadan da Najeriya. A bangaren attajiran ’yan kasuwa kuwa sun yi alkawarin sadaukar da dukiyarsu domin tallafawa kungiyar.