Search
Subscribe
Kungiya ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Giwa

Kungiya ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Giwa

Kungiyar Marubuta ta Majalisar Wakilai (LWF) da ke Abuja ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Giwa, da ke Jihar Kaduna Alhaji Abubakar Shehu da lambar yabo na wanda ya fi dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar a fannin raya tattalin arzikin al’ummarsa tare da samar musu da sana’o’in dogaro da kai.

A yayin da  yake mika lambar yabon a madadin kungiyar a ofishin Shugaban Karamar Hukumar da ke garin Giwa, Sakataren Shirye- Shirye na Kungiyar, Mista Ogwaje Abraham Jomoh, ya ce sun gano haka ne ta hanyar tantancewar da suka yi sakamakon rangadin da suka gudanar a dukkan kananan hukumomin jihar 23.

Ya jinjina wa Alhaji Abubakar Shehu kan yadda yake fifita bukatun al’umma ta yadda za su zauna lafiya ba tare da jin kyashin juna ba da kuma yadda yake gudanar da ayyukan raya kasa.

Da yake amsa tambayoyin Aminiya kan wannan karramawa Kungiyar LWF ta yi masa Alhaji Abubakar Shehu ya ce, irin tsare-tsaren da Allah Ya ba su ikon aiwatarwa ne ya ba kungiyar sha’awa bayan ta ziyarci karamar hukumar, “inda kuma ta jin ta bakin jama’armu da kuma gani da ido da suka yi na irin yadda muke tafiyar da amanar da Allah Ya dora mana ne ya sa suka ba mu wannan lambar yabo,’’ inji shi.

Ya ce su a  karamar hukumar, sun kware ne a kan noma da kiwo, don haka sun hada garmunan huda na shanu guda 100; inda suka zabo matasa hazikai daga kowane yanki na Giwa suka koyar da su yadda ake sana’ar noma don riba bayan koyar da su sun ba su wadannan shanu tare da garmuna domin su inganta sana’arsu ta noma. “Na biyu mun koyar da matan aure 150 yadda ake kiwon zamani tare da samar da awaki 450 muka ba kowace daga cikin matan awaki uku mata biyu namiji daya, domin su yi kiwo. Sai kuma muka koyar da ’yan mata wadanda ba su  ilimin boko 200 sana’ar dinki tare da raba musu kekunan dinkin don su inganta rayuwarsu. Kuma mun taimaka wa magidanta maza da mata masu kananan sana’a su 500 da  jari dubu 10 kowannensu,” inji Shugaban.

Ya yi wa Allah godiya da Ya sa aka fara fahimtar manufarsa, inda ya ce karamar hukumar tasu ta yi iyaka da garuruwan da suke fama da matsalar tsaro da suke jihohin Katsina da Zamfara da Birnin Gwari a Jihar Kaduna, don haka ne suke kokarin inganta rayuwar al’ummarsu da sana’o’i domin bakin da ke shigowa kada su samu damar shiga cikinsu; ganin ba su da sana’ar yi.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin