✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura

Wata daya bayan karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura da ke Jihar Kaduna Dokta Katuka Bege Ayuba da Kungiyar Marubuta ta ’Yan Majalisar Wakilai ta yi,…

Wata daya bayan karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura da ke Jihar Kaduna Dokta Katuka Bege Ayuba da Kungiyar Marubuta ta ’Yan Majalisar Wakilai ta yi, wata kungiyar matasa da ke fafutikar samar da zaman lafiya da shugabanci nagari da ke Minna a Jihar Neja mai suna Nigeria Youth Initiatibe for Peace and Good Gobernance, ta sake karrama Shugaban kan manyan ayyukan da ya gudanar a karamar hukumar.

Yayin mika kyautar karramawar da aka gudanar a ofishinsa a ranar Alhamis din makon jiya, jagoran kungiyar, Kwamared John Jerome Mainasara, ya bayyana Shugaban Karamar Hukumar a matsayin wanda ya tsere sa’a kuma abin koyi ga sauran shugabannin kananan hukumomi na Najeriya baki daya.

Kwamared Mainasara, ya ce ayyukan ci gaban da Shugaban ya samar tare da nasarar samar da zaman lafiya a yankin da a baya ya sha fama da rikice-rikice su suka janyo hankalinsu ga karrama shi domin kara masa kwazo a kan ayyukan da ya sanya a gaba. Ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomin kasar nan su yi koyi da halayensa da suka hada da raya karkara da taimaka wa mata da matasa da kuma samar da zaman lafiya.

Yayin da yake mai da jawabi, Dokta Katuka Bege Ayuba, ya yaba wa kungiyar kan wannan karamci da ta yi masa tare da ’yan majalisarsa, inda ya sadaukar da kambin ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, wanda ya bayyana shi a matsayin kashin bayan samun nasararsa.

Shugaban ya yi kira ga matasa su guji zama karnukan farautar  ’yan siyasar da ba su da kishin kasa, inda ya ce su ci gaba da hada kansu duk da bambancin kabila da addini da su ke da shi domin ci gabansu da na ’ya’yansu da ke tafe da kuma ci gaban kasa baki daya.