Categories: KungiyoyiSana'o'i

Kungiya ta koya wa matasa da mata 200 sana’o’i a Kaduna

Wata kungiyar matasa da ke Gundunmar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta yaye dalibai mata da maza 200 da ta koya wa sana’o’i domin dogaro da kansu.

Daga cikin wadanda aka yaye a makarantar har da wadanda ba Musulmi ba wato mabiya addinin Kirista duk da cewa makarantar tana tsakiyar Musulmi ne.

ADVERTISEMENT

Bikin yaye daliban ya gudana ne a harabar makarantar da ke Titin Kwanar Gurguwa a Rigasa, Daraktan Kungiyar, Malam Abdul’aziz Mohammed Madugu Chanchangi ya ce makarantar ba ta nuna bambancin a tsakanin dalibanta.

Ya ce kusan dukkan wadanda aka yaye ’yan Gundumar Rigasa ce da kewaye kuma hakan na nuna cewa akwai bukatar fahimta a tsakanin Musulmin Rigasa da wadanda ba Musulmi ba da ke gefen Rigasa.

ADVERTISEMENT

Ya ce an koya wa daliban sana’o’i kamar dinki da yin takalma da kwalliya da aski da ilimin kwamfuta sai gyaran wutar lantarki da hada zanen gado na zamani da yin abinci ko girke-girke da sauransu.

“Yanzu haka mun yaye dalibai 200 amma 456 za mu bai wa takardun kammala  makarantar. Manufarmu a matsayinmu na matasan wannan yanki na Rigasa shi ne mu ga cewa matasanmu mata da maza sun samu sana’ar yi domin dogaro kansu,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa wadanda aka yaye da jari wanda hakan zai taimaka su rika  amfani da abin da suka koya.

Shi ma da yake jawabi a wajen, Malam Hussaini Sani, ya bayyana cewa sana’a na da matukar muhimmanci ga rayuwar matasa domin da sana’a magabata suka rayu.

Don haka sai ya bukaci wadanda aka yaye su tabbatar da cewa sun yi amfani da abin da suka koya domin dogaro da kansu.

Ya shawarci iyaye su rika tura ’ya’yansu inda za su koyi sana’o’i ko da kuwa suna zuwa makaranta domin rashin sana’ar hannu ba daidai ba ne.

Sa’annan ya  yaba wa kungiyar matasan da suka kafa wannan cibiyar koyar da sana’o’i tare da yi musu fatan alheri.

. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago