✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta nemi Gwamnatin Jihar Katsina ta maido da ‘yan banga

Kungiyar Wayar da kai kan Kyakkyawan Shugabanci  da Zaman Lafiya da Ci gaba (Awareness for Good Leadership, Peace and Debelopment- AGLPD) ta yi kira ga…

Kungiyar Wayar da kai kan Kyakkyawan Shugabanci  da Zaman Lafiya da Ci gaba (Awareness for Good Leadership, Peace and Debelopment- AGLPD) ta yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya dawo da ’yan sa-kai na ’yan banga cikin aikin dawo da tsaro a jihar.

Kungiyar ta mika bukatarta ce yayin wata zanga-zangar lumana da ta shirya a harabar Masaukin Gwamnan Jihar da  ke Asokoro a Abuja.

A jawabin Shugaban Kungiyar da ya karanta wa ’yan jarida,  Malam Abdullahi Aliyu Katsina, ya ce sun gudanar da taron ne don nuna damuwarsu kan matsalar rashin tsaro a jihar; inda ya bukaci gwamnatin jihar ta dage takukunmin da tasa a kan ’yan banga a jihar.

Ya ce: “Hare-haren da ake kaiwa kan kauyuka a Jihar Katsina sun nuna yadda mutanen jihar suke fama da rashin tsaro wata tara bayan an dakatar da ’yan banga a jihar ba tare da kawo wani mataki a madadin haka ba.”

Kungiyar ta soki gwamnatin jihar kan yin biris da wani rahoton taron da tsofaffin janar-janar na soja da dattawa da manyan ’yan sanda da sauran masu fada-a-ji a jihar suka yi,  inda suka gabatar da matakan tsaro da za a iya dauka wajen inganta tsaro a jihar.

Ya ce: “Wata tara da suka wuce, an yi taron tsofaffin manyan hafsoshin soja da dattawa da manyan ’yan sanda da sauran masu fada-a-ji a Jihar Katsina; saboda samar da tsaro a jihar: amma Gwamnan bai yi aiki da kudirorin da suka gabatar masa ba.”

Takardar korafin da kungiyar ta gabatar ta bukaci, Gwamnan ya bude kofofinsa saboda sauraron korafe-korafen jama’a da shawarwari domin kawo dawwamamen zaman lafiya a jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Gwamnan, Alhaji Abdulkadir Karfi ya karbi takardar korafin kungiyar ta hannun wani ma’aikacinsa, Dahiru Shu’aib, inda ya yi alkawarin mika ta ga Gwamnan Jihar.