✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta nemi hadin kan ‘yan Arewa Mazauna Kurmi

Hadaddiyar Kungiyar ‘yan Arewa Mazauna Kudancin kasar nan a Ikko wacce aka fi sani da kungiyar ‘Gari Ya Waye’ ta ja hankalin al’ummar Arewa mazauna…

Hadaddiyar Kungiyar ‘yan Arewa Mazauna Kudancin kasar nan a Ikko wacce aka fi sani da kungiyar ‘Gari Ya Waye’ ta ja hankalin al’ummar Arewa mazauna Kurmi a kan su farka su hada kai, su zamo tsintsiya daya madaurinki daya.

Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Arewa da su yada dabi’ar nan ta ‘ba zama muka zo ba’, domin a cewar ta wannan halayyar ce ta dakile cigaban ‘yan Arewa mazauna Kurmi tsawon lokaci.

Kungiyar ta bayyana haka ne a yayin bikin karrama daya daga cikin shugabannin ‘yan Arewa, Alhaji Shehu ‘Yar Musa, a Unguwar Hausawa da ke Apapa a Legas a karshen makon jiya.

Shugaban kungiyar, Malam Safwan Sani Zarewa ya shaidawa Aminiya cewa kungiyar ta hinmmatu domin fadakar da al’ummar Arewa mazauna Kurmi domin su farka daga barcin da suke, yana mai cewa lokaci ya yi da ‘yan Arewa mazauna Kurmi zasu farga, su tashi a dama da su cikin abubuwan cigaba a yankunan da suke zaune, suke gabatar da al’amuransu na yau da kullum.

“Mun karrama Alhaji Shehu ‘Yar Musa ne bisa jajircewarsa da taimakon da ya ke yi wa jama’a, domin shi ya farga tun a lokacin iyaye da kakkani, don haka muke so ‘yan Arewa mazauna Kurmi su yi koyi da salon tsarin rayuwarsa, domin shi baya cikin mutanen da ke takaita alkahirin da ya kamata su samu, wato masu dabi’ar nan ta ba zama muka zo ba,” inji shi.

A nasa jawabin, Alhaji Shehu ‘Yar Musa ya bayyana farin cikinsa bisa karramawar da aka yi masa, yana mai cewa zai ci gaba da kokarin da yake na ganin al’ummar Arewa mazauna Kurmi sun ci gaba da samun tagomashi.