✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ASkIN ta kaddamar da sabuwar kalandar lokutan sallah

Kungiyar da ke da manufar fadakar da Musulmi kan lokutan sallah da ganin wata da kuma daidaita alkibla, wadda a Turance ake kira Astro-kibla Initiatibe…

Kungiyar da ke da manufar fadakar da Musulmi kan lokutan sallah da ganin wata da kuma daidaita alkibla, wadda a Turance ake kira Astro-kibla Initiatibe wato (ASkIN), ta gabatar da taron lacca da kuma kaddamar da wata sabuwar kalandar lokutan sallah a matsayin gwaji a karon farko, a karshen makon jiya. 

An gudanar da taron ne a babban dakin lacca na makarantar Almanar da ke farfajiyar masallacin Juma’a da ke mahadar titin Tafawa balewa da na Link Road a Unguwar Rimi, Kaduna
kungiyar, wadda aka yi wa rajista a watan Yulin shekarar 2013 ta himmatu wajen ganin ta gabatar da wadannan muhimman manufofi nata don ganin Musulmi sun fahimci yadda za a gudanar da wadannan shika-shikai na Musulunci kamar yadda ya kamata.
A lokacin da yake jawabi dangane da sha’anin ganin wata, Dokta Hafiz Wali, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ganin wata na kasa, ya tabo takaitaccen tarihin yadda aka fara tun, “Lokacin marigayi Sheikh Abubakar Gumi nake wannan aiki, wanda duk da yadda aka san shi, ake girmama shi, amma ana kiranmu ’yan Kaduna,’ wadansu sai su ce, ‘wadannan sun yi shirka,’ ko ‘kafirai ne’ … yaya ga yadda ake ganin wata… to kuma har yanzu wasu ba su yarda da abin da ake fadi ba. Shi mutum kafin ka canja shi, sai ka nuna masa abu, wanda yake ba yadda zai yi musu. To, in ka nuna wa mutum, ko ya yi musu, ba shi da wani uzuri da zai iya yin wata Magana,” inji shi.
Ya bayyana godiyarsa ga Allah ganin cewa yanzu al’amarin musu dangane da ganin wata ya yi sauki, saboda jama’a sun ganewa, saboda haka ya bukaci a ci gaba da bayar da himma kan wannan fadakarwa da wayar da kai da ake yi.
Sannan ya yaba da yadda aka tsara sabuwar kalandar a cikin hikima, “Musamman da yake tana kunshe da wadansu abubuwa masu yawa da ba su a cikin wadansu kalandun masu kama ta ita. To, idan aka samar da irinta da yawa, za ta yi amfani kwarai,” inji shi.
Shi kuma yayin da yake gabatar da tasa laccar dangane da Alkibla, daya daga cikin’yan kwamitin ganin wata na kasa, wanda masani ne wajen sarrafa na’urar gano ainihin alkibla din, Malam Usman Mahmud ya fara ne da jan hankali kan muhimmancin saisaita alkiblar masallaci ko sabo, ko tsoho. Dangane da haka ne ma ya nuna majigi da wani malami ya yi dangane da wani masallaci mai tarihi da ke San’aa.
Manzon Allah ya umurci daya daga cikin sahabbansa, Wabru ibn Muhannath al-Khuza’iy, ya gina wannan masallacin, kuma ya bayyana masa ya fuskantar da shi wajen wani dutse. Ya aiwatar da umurnin Annabi.
Ya ce wani malami da ke hada shari’a da fasahar kimiyya wajen ciyar da fahimtar da mutane gaba, Sheikh AbdulMajid Alzandaniy ya yi majigin bayanin da ya nuna cewa na’urar ‘Google Earth’ ta kara tabbatar da mazancin Manzon Allah, musamman da yake bai taba zuwa San’aa ba. Aka shata layi da wannan na’ura da ya nuna masallacin yana fuskantar tsakiyar Ka’aba.
A karshe aka kaddamar da kalandar, wadda aka bukaci a duba ta sosai domin tabbatar da ingancin abin da ke cikinta ta yadda nan gaba za a samar da ita sosai kowa ya yi amfani da ita yadda ya kamata