✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Bunkasa Garin Lawanti ta bai wa marayu 256 kayan Sallah

Kungiyar Bunkasa garin Lawanti (Lawanti Community Debelopment) da ke Jihar Gombe, ta faranta wa wadansu marayu rai ta hanyar ba su kayan sallah domin su…

Kungiyar Bunkasa garin Lawanti (Lawanti Community Debelopment) da ke Jihar Gombe, ta faranta wa wadansu marayu rai ta hanyar ba su kayan sallah domin su gudanra da Babbar Sallah cikin walwala.

Da yake jawabi a wajen mika kayan, Shugaban kungiyar Alhaji Abu Ubaida ya ce kungiyar ta saba duk shekara tana ba da irin wannan tallafi ga marayu a lokacin karamar Sallah da kuma Sallar Layya.

Alhaji Abu Ubaida, ya yi kira ga jama’ar jihar, cewa duk mai niyar taimakawa ba sai lallai ya jira kungiyar ba yana iya bayarwa kai-tsaye don samun lada a wajen Ubangiji.

Sai ya yi addu’ar Allah Ya dafa wa kungiyar kan irin wannan aikin madalla da take yi.

Shima ana sa jawabi Malam Sani Aliyu cewa ya yi da duk shekara suna gudanar da irin wannan tallafi ga marayu amma saboda matsin tattalin arziki ba su samu yi a karamar Sallah ba saboda dama daga wajen jama’a suke samun kayayyakin.

Ya ce kayayyakin da suka bai wa marayun sun hada da tufafi da gidajen sauro da Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta ba su.

Ezra Sambo wani dattijo da ya yi magana a madadin masu kula da marayun ya yaba wa kungiyar kan yadda ba ta nuna bambanci addini ko kabila wajen tallafa wa marayun. Sai ya roki Allah Ya taimaka musu Ya biya musu dukan bukatunsu.

Wani mai taimaka wa Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Usman Baraden Lawanti, kira ya yi ga shugabannin kungiyar su toshe kunnensu daga zargin mutane domin duk abin da mutum yake yi don Allah sai wani ya kalubalance shi ya nuna cewa cuta yake yi.

Baraden Lawanti, ya ce baya ga taimakon marayu, kungiyar tana gina makarantu da daukar nauyin karatun yara marasa galihu. Daga nan sai ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da bai wa kungiyar hadin kai da tallafi a duk lokacin da bukatar haka ta taso.

Cikin marayu 256, maza 93 da mata 98 kowane ya samu kayan Sallah da gidan sauro.