Categories: Kungiyoyi

Kungiyar Ci Gaban Funtuwa ta koka kan rashin wutar lantarki a yankin

Kungiyar Ci Gaban Yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina ta koka kan matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da shi a yankin. Shugaban Kungiyar, kuma Limamin Masallacin Gidajen ’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa da ke  Zone B, Apo, Babban Birnin Tarayya Abuja, Imam Ibrahim Awwal [Usama] ne ya bayyana kukan kungiyar, lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce a halin da ake ciki  al’ummar yankin sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rashin wutar lantarki da ake fuskanta a yankin.

ADVERTISEMENT

Ya ce al’ummar yankin sun dogara da wutar lantarki ce wajen gudanar da sana’o’in walda  da  nika da sauran sana’o’i daban-daban, amma saboda rashin wutar; yanzu sun zama ba su samun damar gudanar da wadannan sana’o’i.

Imam Usma ya ce akwai lokacin da masu nikan inji suka yi yajin aiki a yankin, saboda matsalar rashin wutar lantarki.

ADVERTISEMENT

“Kamfanonin da suke rarraba wutar lantarki, babu abin da suka sani, sai  dai su karbi kudin wuta daga jama’a; alhalin ba sa bayar da wutar. Ya kamata kamfanonin da aka bai wa dillacin sayar da wutar lantarki a Najeriya su san mutuncin jama’a,” inji shi.

Ya yi kira ga  Gwamnatin Tarayya ta karbe bayar da wutar lantarki daga kamfanoni masu zaman kansu. Kuma ta tsaya wajen ganin ta samar da tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya wadda al’ummar Najeriya  za su yi amfani da ita, don samun abin da za su dogara da kansu.

Ya yi kira ga  kantomomin yankin Funtuwa da Sanatan yankin da ’yan  Majalisar Tarayya da suka fito daga  yankin Funtuwa su taimaka, su dauki matakan da suka wajaba  don ganin an warware wannan matsala ta rashin wutar lantarki a yankin.

..

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago