✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Corantians ta lashe Kofin Zaman Lafiya na Jos

Kungiyar Kwallon  Kafa ta Corantians da ke Unguwar Rukuba a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato ce, ta lashe Kofin Zaman Lafiya…

Kungiyar Kwallon  Kafa ta Corantians da ke Unguwar Rukuba a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato ce, ta lashe Kofin Zaman Lafiya da Alhaji Abubakar Sadik Plaza ya sanya, bayan da ta samu nasarar jefa kwallo hudu a ragar Kungiyar Kwallon Kafa ta Dutse Uku,  a bugun finareti,  yayin da ta Dutse Uku, ta jefa kwallo uku  a karshen wasan.

Gasar kwallon kafa ta Kofin Zaman Lafiya da Alhaji Abubakar Sadik Plaza ya sanya, kungiyoyin kwallon kafa 20 da suka fito daga unguwannin da Musulmi da Kirista suka fi rinjaye da suke cikin garin Jos da kewaye ne suka fafata. Kuma an shafe wata uku ana gudanar da gasar.

An gudanar da gasar karshe na cin kofin ne a filin wasa na Barikin ’Yan sanda da ke  Duala a garin Jos a yammacin Asabar  da ta gabata.

Da yake mika kofin ga Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Corantians, Alhaji Abubakar Sadik Plaza ya bayyana cewa,  babban abin da ya karfafa masa  gwiwar sanya wannan kofi shi ne domin  ya kawo hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar  Musulmi da Kirista da ke cikin garin Jos da kewaye da Jihar Filato baki daya.

Ya ce  “Muna son  mu nuna wa duniya cewa Allah Ya dawo mana da zaman lafiya a garin Jos, domin a baya kowa yana tsoron ya shiga unguwar da ba tasa ba. Amma  a wajen wannan wasa kowa ya zo daga unguwannin Musulmi da Kirista da ke wannan gari, ba tare da fargaba ko tsoro ba.”

Ya ce nan ba da dadewa ba zai  sake sanya wani babban kofi, na zaman lafiya da za a buga gasar cinsa a babban filin wasa na Jos.

“Babban burina shi ne in ga an samu cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato. Don haka muna rokon jama’a su ci gaba da ba mu goyon baya kan wannan kudiri da muka sanya a gaba. Kuma muna kira ga al’ummar Jihar Filato, kowa ya bada gudunmawarsa wajen ganin an samu tabbatacen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan,” inji shi.