Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar dillalan kayan abinci ta kasa tayi barazanar shiga yajin aiki

Hadaddiyar kungiyar masu hada-hadar kayan abinci ta kasa tayi barazanar shiga yajin aiki biyo bayan yawan haraji da shuwagabannin kungiyar suka ce ana tilasta mambobin kungiyar su biya.

A wani taro da shugaban kungiyar na kasa Dakta Muhammad Tahir ya jagoranta a birnin Uyo na jihar Akwa-Ibom shuwagabannin kungiyar na jihohi da dama sun koka bisa yawan kudin harajin da ake tursasasu su biya akan hanyoyin kasar nan inda suka nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo masu dauki ko kuma su shiga yajin aikin sai baba ta gani, inda za su tsayar da hada-hadar kayayyakin masarufi na abinci kaf wadanda suka hadar da shanu, awaki, tumaki, kayan gwari da daukacin nau’in  kayayyakin abinci a fadin kasar.

ADVERTISEMENT

Kungiyar ta dade tana kokawa bisa yawan shingen karbar haraji akan hanyoyin kasar nan inda a baya ma ta ta a shiga yajin aikin.

ADVERTISEMENT