✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar FOMWAN na ciyar da masu azumi dubu uku a Jihar Bauchi

kungiyar mata musulmi ta Najeriya (FOMWAN), reshen Jihar Bauchi ta bayyana kudirinta na taimakawa wajen ciyar da marayu da magidanta marasa galihu a kalla mutum…

Hajiya Uwani Sani Abubakar, Amirar FOMWAN Bauchikungiyar mata musulmi ta Najeriya (FOMWAN), reshen Jihar Bauchi ta bayyana kudirinta na taimakawa wajen ciyar da marayu da magidanta marasa galihu a kalla mutum dubu uku a cikin garin Bauchi da yankunan kananan hukumomi na jihar a cikin wannan wata na Ramadan.
Hajiya Uwani Sani Abubakar, Amirar kungiyar ta bayyana haka cikin hirarta da wakilinmu, inda ta kara da cewa shekaru da dama suke taimakawa musulmi, musamman marayu da marasa galihu da magidanta da ba su da halin sayen abinci su kai gidajensu. Ta ce suna dafa abincin ne su raba a masallatan cikin garin Bauchi da yankunan kananan hukumomi saboda neman tubarrakin da ke cikin watan Ramadan.
Ta ce duk da karancin kudi suna kokarin ciyar da iyalan da suka kawo koke gare su ta hanyar sayen abinci suna raba wa matalauta da kuma gidajen da aka rasu aka bar marayu, suna bayar da mudu uku zuwa biyar na shinkafa da kuma suga mudu biyu  da sauran abin da ya samu ga kowane mutum da suke tallafa wa.
Ta ce suna ciyar da kimanin mutane dubu da dari biyar a cikin garin Bauchi kurum, haka a kananan hukumomi suna ciyar da wannan adadi bisa jimlar kiyasin da a kullum suke ciyar da a kalla mutane dubu uku a masallatai da wanda ake kai wa gidajen wadanda ba su da shi.
Daga karshe Amira Uwani Sani ta shawarci mata su kasance masu biyayya da hakuri game da dan abin da mazaje suka kawo gida. “A kauda dabi’ar rashin godiya saboda wannan lokaci ne da maza suke shan wahala wajen dawainiyar gida. Don haka mata su nemi ladar dawainiyar gida da suke yi wajen Allah, su sani kowa a wannan lokaci hakuri yake yi da yadda ya samu rayuwa. Su kasance masu neman abin kansu kar su dogara dungurungum a kan mazaje, su ma su tallafa ta wani gefen”. Inji ta.