✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Fulani ta dauki matakin magance satar shanu a Kudu

Kungiyar Ci gaban al’ummar Fulani (GAFDA), wacce ke gudanar da al’amuranta a Kudu Maso Yamma ta ce ta kafa wani ayari na yaki da satar…

Kungiyar Ci gaban al’ummar Fulani (GAFDA), wacce ke gudanar da al’amuranta a Kudu Maso Yamma ta ce ta kafa wani ayari na yaki da satar dabbobi da lalubo hanyar magance rikici a tsakanin manoma da makiyaya a yankin. “Kungiyar ta samu amincewar kafuwar ayarin daga gwamnatocin jihohi shida na sashin,” inji Kakakin Kungiyar, Alhaji Isa Adamu.

Da yake yi wa ’yan jarida bayanin sakamakon taron da kungiyar ta yi a Ibadan, Isa ya ce “Sabon sashin yaki da satar dabbobi da muka kirkiro zai rika shiga cikin kauyukan da Fulani suke zaune da dabbobinsu ne domin lura da kai-kawon barayin dabbobi a kowace karamar hukuma a wannan sashi. Kungiyarmu ta GAFDA ta umarci ayarin da ya yi kokarin ganin ya kama duk wanda ake zargi da satar dabbobi da tabbatacciyar shaida tare da mika shi ga jami’an tsaro, ba tare da cin zarafin kowa ba. Muna ganin daukar wannan mataki zai taimaka wajen dakile ayyukan barayin shanu.” Ya kara da cewa, “Yanzu haka kafa wannan ayari ya sa irin wadannan barayin shanu sun fara gujewa daga wuraren da suke zaune zuwa wasu sassan kasar nan. Za mu yi aikin ba sani ba sabo wajen tabbatar da doka ta yi aiki musamman a kan Fulanin da ake hada baki da su ana cutar da ’yan uwansu.”

A game da matsalolin rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci ya ki cinyewa sai ya ce, “Babbar kungiyarmu ta sadaukar da kanta wajen gudanar da aikinta tsakani da Allah, musamman wajen yin amfani da sarakunan Fulani da kungiyoyinsu da aka dora musu alhakin hanzarta yanke hukuncin biyan diyya ga manoman da dabbobinmu suka lalata musu amfanin gona. Sai dai abin bakin ciki shi ne, muna biyan diyyar amfanin gona da aka lalata amma ba a biyanmu diyyar dabbobin da aka kashe mana. Wannan ne ya sa muka yi wannan taro domin tattaunawa a kan yadda za mu fuskanci wannan lamari.”

Kakakin Kungiyar GAFDA ya ci gaba da cewa, “Muna murna da dawowar zababben Gwamnan Jihar Ekiti Dokta John Kayode Fayemi, wanda a lokacin mulkinsa na farko ya tabbatar da nada Alhaji Abashe Adamu a matsayin Sarkin Fulanin Jihar Ekiti. Kuma Gwamna Fayemi ne ya kirkiro hanyar zama bisa teburi daya a tsakanin ofishinsa da bangarorin manoma da makiyaya da suke tattaunawa a kan matsalolin da suka shafe su. Shi ma zababben Gwamnan Jihar Osun Alhaji Gboyega Oyetola, muna fatan zai ci gaba da gudanar da aikin tsaron lafiyar Fulani da dabbobinsu kamar yadda Gwamna mai barin gado Ogbeni Rauf Aregbesola ya faro.”

Kakakin ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarin da gwamnatinsa take yi game da al’amuran tsaron kasa. Ya yi addu’ar rokon Allah Ya wargaza muguwar aniyar wadansu ’yan siyasa da suke amfani da matsalar rikicin manoma da makiyaya wajen cimma burinsu na hargitsa kasa.