✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Gizago ta ziyarci Kamfanin Daily Trust

A jiya Alhamis Ce Kungiyar Gizago ta Kasa ta kawo ziyara Hedkwatar Kamfanin Media Trust mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja.…

A jiya Alhamis Ce Kungiyar Gizago ta Kasa ta kawo ziyara Hedkwatar Kamfanin Media Trust mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja.

Da yake jawabi lokacin ziyarar, Shugaban Kungiyar ta Kasa Alhaji Kabir Adam Gombe ya ce wannan ne karo na biyu da ’ya’yan kungiyar suka kawo ziyara gidan jaridar bayan kafa kungiyar a shekarar 2009.

Shugaban ya zayyana ayyukan da kungiyar ke gudanarwa a shekara 10 da kafuwarta da suka hada da kai ziyara gidajen marayu da bayar da tallafi ga ’ya’yan kungiyar lokacin bukukuwan aure ko suna da hada mu’amalar kasuwanci tare da kulla zumunci a tsakanin mambobin kungiyar. Ya ce sun yi nasarar hada aure a tsakanin mambobin kungiyar biyar.

“Mun saka taron kasa da muka saba gabatarwa duk shekara, amma sama da wata takwas uwar kungiya ta kafa kwamitin taron kasa, saboda gudanar da taron, amma abin ya ci tura sakamakon rashin kudi,” inji shi

Ya bukaci taimakon Kamfanin Media Trust don dafa wa ayyukan kungiyar ta fuskar kara ba su goyon baya da tallafin kudi tare da tallata kungiyar don samun tallafi daga gwamnati ko manyan kungiyoyi na ciki da waje masu taimakon ayyukan kungiyoyi masu zaman  kansu don su ma su taimaka wa jama’a, ta hanyoyi daban-daban.

A tsokacin Editan Jaridar Aminiya, Salihu Ibrahim Makera, ya jinjina wa shugabannin kungiyar ta Gizago bisa hadin kai tare da tallata jaridar ta Aminiya da suke yi. Sai ya yi kiran su ci gaba da hada gwiwa da Kamfanin Media Trust, don a gudu tare a tsira tare.

Tun farko, Manajan Editan Kamfanin wanda jagoranci tarbar bakin, Malam Nasir Lawal Abubakar ya nuna jin dadinsa kan wannan ziyara da suka kawo, sannan ya  yi musu alkawarin cewa za a duba bukatunsu don daukar mataki a kai.