✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Hausa Fulani ta Jihar Borno ta samu rajista

Kungiyar Hausa Fulani Debelopment Association ta samu rajista, inda ta gabatar da takardar rajistar a wani taron da ta gudanar a Cibiyar ’Yan jarida ta…

Kungiyar Hausa Fulani Debelopment Association ta samu rajista, inda ta gabatar da takardar rajistar a wani taron da ta gudanar a Cibiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Borno a Maiduguri. Gabatar da rajistar ya samu halatar daruruwan ’ya’yan kungiyar daga sassan  jihar.

Da yake jawabi, Sakataren Kungiyar, Alhaji Aminu Gwandu, ya ce hakika kungiyar ta sha gwagwarmaya kafin ta kai halin da take ciki a yanzu. Ya ce tun kafin samun rajistar kungiyar tana aiwatar da ayyukan bunkasa rayuwar al’umma a fannoni daban -daban, kamar sa yara marayu a makaranta da tallafa wa ’ya’yan kungiyar da kuma bada gudunmawa wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a Jihar Borno da kasa baki daya.

Sai ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su kasance masu bin  doka, tare da tabbatar da kowa yana da sana’ar yi.

Alhaji Aminu Gwandu, ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Borno ta mara wa kungiyar baya, domin samun ci gaban da ake bukata. Ya ce kungiyar ta kai ziyara gidan yari na Maiduguri da ke Unguwar State Low Cost, inda ta kai kayan tallafi ga wadanda suke tsare.

Tun farko a jawabin Shugaban riko na kungiyar, Alhaji Muhammad Tuta Habib, kira ya yi ga ’ya’yan kungiyar su guji zaman banza, su kuma yi riko da sana’a komai kankantarta. Ya bai wa ’ya’yan kungiyar tabbacin yin duk abin da ya dace domin ganin kungiyar ta zama tsintsiya madaurinki daya, inda ya yi kira ga sauran kungiyoyin da ke jihar su mara wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum baya, wajen yi masa addu’a domin samun ingantaccen zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Daya daga cikin shugabannin da aka bai wa takardun shaidar, Shugaban Kungiyar na Karamar Hukumar Maiduguri, Malam Hussaini Abubakar Soja, ya bayyana farin cikinsa, inda ya yi kira ga jama’a su mara wa kungiyar baya. Kuma ya tabo jerin ayyukan da kungiyar ta fara aiwatarwa na sama wa yara gurbin karatau a Jami’ar Maiduguri da samar da guraben aiki ga wadanda suka kammala karatu. Ya ce za su bude wata gidauniya ta agaza wa duk  dan kungiyar da bukatar tallafa masa ta taso.