✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar  Interfaith ta shirya bita kan yaki da cin hanci da rashawa

Kungiyar Tattaunawa a Tsakanin Addinai  mai zaman kanta (Interfaith Mediation Centre – IMC) da ke Kaduna ta gudanar da taron yini guda ga shugabannin addinai…

Kungiyar Tattaunawa a Tsakanin Addinai  mai zaman kanta (Interfaith Mediation Centre – IMC) da ke Kaduna ta gudanar da taron yini guda ga shugabannin addinai da ’yan siyasa da sauran masu ruwa-da-tsaki kan yadda za a shawo kan cin hanci da rashawa tun daga tushe a cikin al’umma ta hanyar gudunmawar shugabannin addini da na siyasa da kuma sarakunan gargajiya za su bayar.

Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Karamar Hukumar Jama’a da ke garin Kafanchan, an tattauna dalilan da suke haifar da cin hanci da rashawa da illolinsu a cikin al’umma da kuma dalilan da suke kawo tsaiko wajen magance matsalar wadda take addabar mutanen Najeriya.

Da yake gabatar da jawabi a ranar Asabar da ta gabata kan manufar taron mai taken ‘Rawar da Shugabanni da Malaman Addini Za Su Taka Wajen Yaki da Cin Hanci da Rashawa’, Daraktan Kungiyar IMC, Dokta James Wuye, ya ce suna son samar da wata mahada ce da mutane za su hadu tare da zababbun ’yan siyasarsu don tattauna yadda za a rage mummunar dabi’ar nan ta cin hanci a kasar nan.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Imam Muhammad Nuraini Ashafa, ya ce sun shirya taron ne domin nemo yadda za a magance matsalar da ta yi katutu ta hanyar daidaiku da kuma kungiyoyi kan abubuwan da ke haddasa cin hanci da rashawa a cikin kasa.

Yayin da suke ba da gudunmawarsu kan dalilai da kuma yadda za a shawo kan lamarin, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Karamar Hukumar Jama’a, Rabaran John Mark da takwaransa na Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, Alhaji Ilyasu Musa, sun bayyana jin tsoron Allah da tona asirin masu aikata laifin a cikin al’umma tare da hukunta su a matsayin wasu daga cikin hanyoyin da za su rage yaduwar matsalar.

A cewar Rabaran Mark, dole ne al’umma ta tashi tsaye wajen yaki da wannan muguwar dabi’a don kare zuriyar da ke tafe da dandana kudarsu ta hanyar girbe abin da ba su suka shuka ba.

Shi ma Alhaji Ilyasu Musa na JNI, ya koka kan yadda Musulmi da Kirista suka dauki littattafansu ababen rantsuwa yayin kama aiki yayin da ba sa muhimmantar da karantarwar da ke cikin littattafan.

Wakilan kungiyoyin Musulmi da Kirista da ’yan siyasa da wakilan Sarakunan gargajiya ne suka halarci taron.