✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Izala ta baiwa mata jari bayan koyar da su sana’a a Abuja

A ranar Asabar da ta gabata ce Kwamitin Tallafa wa Marayu da Zawarawa na Kungiyar Izala ta Abuja ya koyar da zawarawa sana’ar girki da…

A ranar Asabar da ta gabata ce Kwamitin Tallafa wa Marayu da Zawarawa na Kungiyar Izala ta Abuja ya koyar da zawarawa sana’ar girki da kayan sha na marmari  a harabar Masallacin Juma’a na Berger da ke Utako a Abuja.

Bayan koyar da sana’o’in, kwamitin ya danka wa matan jari da na’urorin hada kayan abincin don komawa gida su ci gaba da sana’a don taimaka musu wajen kula da ’ya’yansu marayu da mazansu suka rasu suka bar su da su.

Sakataren Kwamitin, Alhaji Muhammad Sani Jebba ya ce wannan ne karo na biyar da kwamitin ya shirya irin wannan bita don koya wa  zawarawa mata sana’o’in dogaro da kansu. “A baya mun koyar da su yadda ake yin sabulai da garin sabulun wanki da man shafawa da sinadaran yaki da kwayoyin cuta da sauransu, amma a wannan karo mun ga dacewar mu sauya akala zuwa fannin girke-girke na zamani da ake sayarwa a manyan kantuna da gidajen abinci,” inji shi.

“Mun gudanar da wannan bita ce a kananan hukumomi biyu, wato Birnin Abuja (AMAC) da Gwagwalada wadda ta kunshi mata 150. Kuma mun kashe fiye da Naira dubu 500, inda muka koya musu irin su yadda ake Samosa da man kwakwa da gyada da soya plantain da ganyen shayi da kori da sauransu. Kuma mun ba wadansu daga cikinsu jarin Naira dubu 10 kowace, wadansu kuma muka ba su na’urorin hada kayayyakin” inji Jebba.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Sa’idu Musa Yelwa ya ce kwamitin zai kara dukufa kan wannan aiki sakamakon yadda matan da mazansu suka rasu ke shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi. Sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyi su shiga cikin irin wadannan ayyuka na jinkai don neman yardar Allah da kuma martaba rayukan masu rauni a cikin al’umma.

Malama Hauwa Inuwa tana daya daga cikin malaman da suka koya wa zawarawan sana’o’in kayan tande-tande da lashe-lashe na zamani, ta ce ba su samu wata matsala wajen koyar da matan ba duk da cewa wadansu daga cikinsu sun haife su. Ta ce za ta ci gaba da ba da hadin kai don tabbatar da cewa mata sun samu hanyoyin dogaro da kansu.

Hajiya Rukayya Hussaini, Shugabar Cibiyar Back To Books Initiatibe wadda ta halarci taron, ta nuna jin dadinta kan yadda ta ce ta ga matan da aka koyar da su sana’o’in suna murna da farin ciki, bayan karbar tallafin da aka ba su. Sai ta bukaci jama’a su taimaka ba tare da raina abin da zasu bayar ba.