✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Izala ta shirya wa ’yan takara bita a Gombe

A lokacin da babban zaben bana ke kara karatowa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Gombe ta shirya wa ’yan takarar mukamai daban-daban…

A lokacin da babban zaben bana ke kara karatowa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Gombe ta shirya wa ’yan takarar mukamai daban-daban bita don fadakar da su.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Kungiyar ta Jihar, Injiniya Salisu Muhammad Gombe, ya ce Izala ta shirya taron ne don fadakar da ’yan takara kan hakkin da ya rataya a kansu bayan sun ci zabe.

Ya ce, siyasa za ta zo ta wuce ta bar mutane, don haka ake son ilimantar da ’yan takarar kan muhimmancin zaman lafiya da ci gabanJihar Gombe.

Injiniya Salisu Gombe ya kara da cewa, Izala ta shirya wani taro makamancin wannan ga matasa da ke amfani da shafuffukan sada zumunta na zamani don su kauce wa sukar juna da kalamai na batanci saboda ’yan siyasa.

Shugaban ya kara da cewa, kafin zaben, kungiyar za ta sake shirya wani taro na mata don wayar da kansu kan muhimmancin kada kuri’a da kuma fitowa zabe domin mafi yawan kuri’un da ake samu a lalace lokacin zabe na mata ne.

A jawabin Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Garba Sarkin Malaman Pantami, ya ce a matsayinsu, na shugabanin jam’iyyun siayasa ba za su zuba ido suna ganin wani dan takara yana lalata matasa ta hanyar bangar siyasa ba.

Sarkin Malaman Pantami, ya ce a karkashin kungiyarsu ta IPAC sun yi zama da ’yan takara sun yi yarjejeniya a kan ba wani dan takara da zai bar magoya bayansa su dauki makamai a lokacin yakin neman zabe don razana mutane, kuma duk dan takarar da magoya bayansa suka yi haka za a sa hukumar zabe ta dakatar da shi.Babban Bako na Musamman Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III wanda ya samu wakilcin Durbin Gombe Alhaji Lamido Abubakar, ya jinjina wa kungiyar Izalar ce bisa shirya wannan taro ga dukan ’yan takara a kowane mukami.

Sarkin Gombe ya yi kira ga dukan ’yan takarar, su gudanar da kamfe cikin kwanciyar hankali l domin in ba zaman lafiya zaben ma ba zai gudana yadda ya kamata ba.

Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Umar, wanda Baturen Zabe na Karamar Hukumar Gombe, Alhaji Ibrahim Ali ya wakilta ya yi kira ga sauran kungiyoyin addinai, su yi koyi da kungiyar Izala wajen shirya irin wannan taron fadakarwar.

’Yan takara da dama da suka yi jawaban godiya sun nuna gamsuwa kan yadda kungiyar ta Izala ta shirya musu wannan taro.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Jami’a Jihar Gombe ya samu halartar ’yan takara da dama maza da mata da suka hada da ’yan takarar gwamna da na majalisun jiha da tarayya daga jam’iyyu daban-daban.