Search
Subscribe
Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe ta jaddada goyon baya ga Shugaban Majalisar Dattawa

Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe ta jaddada goyon baya ga Shugaban Majalisar Dattawa

Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe ta tabbatar da niyyarta ta kara goya wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan baya,  bisa ga taimakon da yake ba kungiyar.

Shugabar Kungiyar Kansilolin ta Forum for Yobe State Councillors, Hajiya Hafsat Alhaji Ado, Kansila mai wakiltar Damaturu ta Tsakiya ta bayyana haka lokacin da take zantawa da Aminiya inda ta ce Sanata Ahmed Lawan dattijo ne mai adalci.

Ta ce dattakun Sanata Ahmed Lawan ya sa aka zabe shi ya zama Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan jiharsu ce ta Yobe shi ya sa suke kara jinjina masa.

Shugabar ta ce suna alfahari da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa inda yake kokari wajen yi wa jiharsa da mazabarsa ayyukan raya kasa.

Ta kara da cewa yanzu haka ya kawo tallafi a mazabarsa don taimaka wa matasa da al’ummarsa saboda su amfana kuma su shaida ribar mulkin siyasa.

Daga nan sai ta yi fatan alheri da kuma rokon Allah Ya sa ya gama lafiya ya kuma samu ikon sauke nauyin da ke kansa.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin