✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar KKDA ta karrama ‘ya’yanta da suka samu mukamai

Kungiyar Ci gaban Unguwar Kumbiya-Kumbiya (KKDA) da ke garin Gombe ta karrama ’ya’yanta bakwai da suka zama kusoshin gwamnati a matakai daban-daban. Kumbiya-Kumbiya unguwa ce…

Kungiyar Ci gaban Unguwar Kumbiya-Kumbiya (KKDA) da ke garin Gombe ta karrama ’ya’yanta bakwai da suka zama kusoshin gwamnati a matakai daban-daban.

Kumbiya-Kumbiya unguwa ce a Gombe; da take da dadadden tarihin, inda bayanai suka ce an kafa ta ce a 1919.

An ce sunan unguwar na Kumbiya-Kumbiya, ya samo asali ne daga unguwar baki saboda akwai wajen da ake kira zango inda masu sayar da goro suke yada zango idan suka je Gombe, kuma Sarkin Gombe na wancan lokaci ne ya yi umarnin a kai su zangon.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Kungiyar KKDA ta Kasa, Dokta Yerma Adamu, wanda tsohon Kwamishinan Lafiya ne a jihar a gwamnatin ANPP ta marigayi Alhaji Abubakar Habu Hashidu, ya ce an kafa kungiyar ce a 1992 da mutum uku har ta kai 1997 ana ayyukan ci gaban unguwar inda wadansu suka fara shiga siyasa ta dalilin kungiyar.

Dokta Yerma Adamu, ya ce a shekarar 2006 dattawan unguwa suka sake zama suka kaddamar da ita aka ce shi Dokta Yerima ya shugabance ta inda shi kuma ya gindaya sharuddan duk mai son zama mamba sai ya ajiye ra’ayin siyasa da bambancin addini da kabilanci.

Ya ce sun yi aikace-aikace na fiye da Naira miliyan 30 a shekara 27 da kafuwarta ciki har da gina ajin yaki da jahilci da marigayi Malam Yerima ya gina har wajen ya zama Islamiyya da aka samu mahaddatan Alkur’ani Mai girma, sannan sun gina makaranta da ban-daki da kudinsu ya kai Naira miliyan tara da kuma kwalbati a kusa da shagon littafai na A.A Haruna.

“Kungiyar KKDA ta inganta cibiyar lafiya ta Kumbiya-Kumbiya ta samar mata da magunguna da kayayyakin aiki; inda yanzu haka muke shirin sayen wani gida da ke gabas da asibitin don gina shi ya hade da asibitin ya zama dakin kwantar da mata marasa lafiya, kuma niyyarmu ita ce ya zama babban asibiti nan gaba,” inji Yerma.

Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya FCE (T), da ke Gombe Dokta Ali Boderi, ya gode wa kwamitin da suka shirya wannan karramawa kan yadda suka zakulo su suka karrama su bayan zamansa shugaban kwalejin da shekara daya.

Dokta Ali Boderi, ya ce yana da kyau iyayen kungiyar su rika ba su shawarwarin da suka kamata don kara dora su a hanya.

Yeriman Gombe Hakimin Cikin Garin Gombe da Kewaye Alhaji Abdulkadir Abubakar, kira ya yi da jan kunne ga al’umma kan su yi koyi da irin hadin kan da mutanen Unguwar Kumbiya-Kumbiya suke da shi.

Sannan ya ja hankalinsu kan su ci gaba da taimakon al’umma kamar yadda suka faro musamman a bangaren ilimi domin shi ne tushen rayuwa sannan su rungumi juna wajen samar wa yara aikin yi.

Wadanda aka karrama sun hada da Babban Safiyo na Jihar Gombe Zakari Abubakar Difa da Bala Sani Darakta a Asibitin Koyarwa na Tarayya da Malam Ibrahim Abubakar Difa Mataimakin Magatakardar Jami’ar Jihar da Usman Kamara Sakataren (PPS) Gwamna Inuwa Yahaya da Muhammad Kabir Usman Kukan-Daka,  Kwamishina a Hukumar Rabon Tattalin Arzikin Kasa da Malam Abdullahi Suleiman Magatakardar Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Kumo da kuma Dokta Ali Boderi Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gombe.