✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Likitoci ta dakatar da yajin aiki bayan Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga tsakani

Bayan shiga tsakani da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, Kungiyar Likitoci karkashin National Association of Resident Doctors of Nigeria (NARD) ta dakatar da…

Bayan shiga tsakani da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, Kungiyar Likitoci karkashin National Association of Resident Doctors of Nigeria (NARD) ta dakatar da shiga yajin aikin da ta yi niyyar farawa.

Kungiyar dai ta sanar ne bayan Babban Taron ta karo na 39 a Jihar Edo a watan Mayu cewa ta ba da wa’adin kwana 40 ko a biya basussukan da suke bin gwamnati, ko su shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Bayan wa’adin ya cika, sai Shugaban Majalisar Wakilai ya bukaci su dakatar da shirin da suke yi na shiga yajin aikin, sannan su ba shi lokaci domin ya nemo bakin zaren.

Shugaban kungiyar, Olusegun Olaopa ya ce sun dakatar da shiga yajin aikin ne domin su girmama maganar Shugaban Majalisar, sannan kuma su ba shi dama ya gudanar da abin da ya yi niyya