Da Dumi Dumi

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Jihar Jigawa ta kaddamar da ofishinta

Gwamna Badaru na Jihar Jigawa

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Kasa Reshen Jihar Jigawa ta kaddamar da ofishinta da ta gina a kan titin bayan Gidan Rediyon Jihar Jigawa da ke Unguwar, G-9.

Kungiyar ta ce ta kashe Naira miliyan 5 da dubu 912, kuma an gina cibiyar ce ba tare da wani tallafi daga Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu ba.

Shugaban Kungiyar, Malam Maharazu Muhammad, ya bukaci gwamnatin jihar ta tallafa musu da kudin da za su sayi kayan kawata ofishin da suka hada da kujeru da Projector da na’urar sanyaya dak, da kayan wuta da firiza.

Ya kara da cewa da kansa ya sayi filin da aka gina sabon ofishin kungiyar tun jihar Jigawa tana sabuwa; kimanin shekara 25 da suka gabata,  a kan Naira dubu 130.

Ya ce a duk Najeriya, babu inda kungiyar take da ofishi makamancin na jihar. Sa’annan ya gode wa gwamnatin jihar wajen biyan ma’aikatan lafiya hakkokinsu na karatu da sauran hakkokinsu, inda ya ce gwamnatin ta kashe sama da Naira miliyan 110, wajen biyan ma’aikatan lafiya hakkokinsu.

ADVERTISEMENT

Ya ce abin da ya fi damun kungiyar, shi ne karancin kudi da za ta gudanar da ayyukanta, sai ya bukaci gwamnatin jihar ta kara daukar ma’aikatan lafiya a dukkan  asibitocin jihar saboda karancin ma’aikatan lafiya a jihar, musamman ma’aikatan jinya da ungozoma.

Shugaban Ma’aikatan Jihar, Malam Nuhu Alhassan Kila, ya ce Gwamnatin Jihar ta kashe magudan kudade wajen gina asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da asibitocin kwararru da makarantun kiwon lafiya a sassan jihar don inganta harkar kiwon lafiya.

Share