Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar malaman kwalejin ilimi ta janye yajin aiki

Kungiyar malaman kwalejin ilimi ta Najeriya (COEASU) ta janye yajin aikin gama gari da take yi na sama da wata biyu.

Shugaban kungiyar COEASU Nuhu Ogirima, ne ya bayyana wa manema labarai hakan jiya Laraba a Abuja, inda ya ce sun dauki matakin janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da masu fada aji na kasa.

ADVERTISEMENT

Ya kuma ce, janye yajin aikin ya zama wajibi ne bayan kyakkyawan zaton da suke da shi daga wurin gwamnati don biya wa malamai bukatunsu.

ADVERTISEMENT