Da Dumi Dumi

Kungiyar masu Dankalin Turawa na fuskantar matsaloli a Jihar Katsina 

Shugaban Kungiyar Nura Aliyu
Shugaban Kungiyar Nura Aliyu

Kungiyar masu sayar da Dankalin Turawa ta Jihar Katsina ta ce tana fuskantar matsalolin da suke hana tafiyar da ayyukan kungiyar kamar yadda ya kamata.

Shugaban Kungiyar Nura Aliyu ya ce, manyan matsalolin da suke fuskanta sun hada da rashin hadin kai daga bangaren shugabanni wanda hakan ya shafi sauran mambobin kungiyar.

Ya ce, “Kin bin doka daga mambobi wanda ya hada da kin biyan kudin ka’ida wadanda da su ne ake tafiyar da harkokin kungiyar. Sa’an nan a duk lokacin da muka yanke wata shawara musamman a wajen sayen kaya domin samar wa jama’a sauki musamman a lokacin watan azumi, sai a samu wadansu su zagaye su yi abin da suke so. Kayan nan mun san inda muke sayo su da hannun wadanda muke sayen, amma waccan matsalar ta kin bin shawarar take sanyawa dole a sayar da tsada saboda an sayo da tsadar bayan kuma ga yawaitar mabukata ga karancin kayan,” inji shi.

Shugaban ya ce akwai masu yi musu kutse a harkokin kungiyar da kasuwancin; wanda hakan ba karamar illa ba ce a harkokin kowace irin kungiya.

Sannan ya ce ba su samun goyon baya daga gwamnati, inda ya bayar da misali da tallafin da suka taba nema inda a karshe  aka gaya musu cewa ko da za a ba su gudunmawar sai sun shiga karkashin wata kungiyar wadda su kuma suke ganin duk matsayinsu daya ne.

ADVERTISEMENT

Ya ce kungiyar tana da  mambobin da suka haura dubu uku a yankunan uku shiyyar Daura da Funtuwa da kuma Katsina.

Shugaban ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su hada kai domin magance wadannan matsaloli, ganin yadda sana’ar da harkokin kungiyar suke da muhimmaci musamman ta lura da yadda zamani ke tafiya. “Yana da kyau mu san cewa, kowace irin gudunmawa muke nema daga ko’ina sai muna da hadin kai za mu same shi. Mu dubi yadda muke da abokan mu’amala; hatta daga makwabciyar kasarmu, amma yau muna gani suke zagayewa saboda rashin hadin kanmu. A kan haka nake kira mu yi kokarin kawar da duk abin da muka san shi ke kawo mana matsala domin samun ci gabanmu,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta samar masu wurin da za su rika ajiyar kayansu tunda a yanzu ana noman dankalin a jihar. Kuma ya nemi manyan ’yan kasuwar jihar su rika shigowa sashensu wanda hakan zai taimaka wajen habaka kasuwanci tare da harkokin kungiyar.

Share