✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar masu sayar da katako ta sami sababbin shugabanni

kungiyar masu sayar da katako a Jihar Gombe ta rantsar da sababbin shugabanin da za su ja ragamarta na tsawon shekaru hudu.A jawabinsa, Kwamishinan Matasa…

kungiyar masu sayar da katako a Jihar Gombe ta rantsar da sababbin shugabanin da za su ja ragamarta na tsawon shekaru hudu.
A jawabinsa, Kwamishinan Matasa da Rage Radadin fatara na jihar, Alhaji Mijinyawa Sani Labaran, ya nuna farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben.
Kwamishinan, wanda Ahmad T. Bojude ya wakilce shi, ya yi kira ga sauran kungiyoyi su yi koyi da ’yan kungiyar masu sayar da katakon. Daga nan sai ya hori sababbin shugabanin su yi jagorancin da ya kamata, yadda za a yi koyi da su nan gaba.
Shi kuwa Uban kungiyar, wanda shi ne Hakimin cikin garin Gombe da kewaye, Alhaji Abdulkadir Abubakar, shawartar shugabanin ya yi da su rungumi kowa, a tafi tare wajen tafiyar da shugabancinsu, kada su sa son rai da zai sa a sami rashin jituwa a tsakaninsu. Kada su yi almubazzaranci da kudaden kungiyar, kuma su kasance masu bai wa shugaba shawarwarin da suka dace.
Hakimin ya jinjina wa Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo bisa tallafin da ya bai wa ’ya’yan kungiyar a lokacin da suka gamu da wata jarrabawar gobara.
Daraktan hukumar wayar da kan al’umma ta kasa, reshen jihar, Mista Ado Solomon, jinjina wa ’ya’yan kungiyar ya yi bisa yadda suke tafiyar da ita cikin hadin kai da kaunar juna. Saboda haka ya hore su da su kawar da duk wani bambanci a tsakaninsu, wanda zai iya raba kansu, su rungumi harkar kasuwanci da hannu bibbiyu.
A nasa tsokaci, shugaban masu kanana da matsakaitan sana’o’i, Alhaji Yusuf Haruna,  kiran ’yan kungiyar ya yi kan su yi kokarin samun ilimin yadda za su dinga sarrafa dussar katakon, wanda ake yin silin da kofofi irin na zamani da shi.
Sabon shugaban kungiyar, Alhaji Babayo Habibu godiya ya yi ga Allah sannan da yadda ’ya’yan kungiyar suka ba shi goyon baya ya ci zaben. Ya gode wa tallafin Gwamna dankwambo ya ba kungiyar.  Daga nan ya bukaci mambobin kungiyar su ba shi hadin kai da shawari nagari don a samu ciyar da kungiyar gaba.
Barista P.K. Gayus da Barista Rejoice Shu’aibu su ne suka rantsar da sababbin shugabannin a zauren taro na makarantar koyon aikin jinya da unguzoma.
Cikin wadanda aka zaba akwai Alhaji Sule Maikatako, Sarkin Yakin Kirfi a matsayin mataimakin shugaba; sai Alhaji Musa Yahaya Bashir, a matsayin sakatare.