Da Dumi Dumi

Kungiyar Mata ’Yan Tijjaniya ta koyar wa mata 300 sana’o’i

Shugabar Kungiyar Mata Musulmi Mabiya Darikar Tijjaniya ta Najeriya (Tijjaniya Muslim Women Debelopment Association) Sayyada A’isha Mai Diwani, wacce aka fi sani da Sayyada Alaika, ta ce sun koya wa mata 300 sana’o’i a Gombe.

Ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da Aminiya a Gombe bayan wani taron wuni guda da kungiyar ta yi.

Shugabar ta ce an kafa  kungiyar ce domin fadakar da mata Musulmi da kuma wa’azantar da su  da zimmar samun hadin kai cikin sauki da kuma koya musu sana’o’i.

Ta ce kungiyar ta kai shekara uku da kafuwa kuma cikin wadannan shekaru ta koyar da mata da dama sana’o’in hannu daban-daban a duk fadin Najeriya.

Baya ga koyar da sana’a ta ce, kungiyar tana taimaka wa mambobinta mata Musulmi idan suka samu jarrabawar rayuwa, sannan sukan yi ziyarci gidajen marayu da asibitoci da kuma gidan yari don kai musu tallafi.

ADVERTISEMENT

Sayyada A’isha Alaika, ta ce cikin sana’o’in da suke koya wa mata akwai dinki da rini da saka da matsar man gyada da sauran sana’o’in mata na cikin gida don su samu su taimaka wa kansu.

Har ila yau ta ce kamar matan da mazansu suka rasu ma suna amfana da  kungiyar domin kungiyar takan dauke musu dawainiyar makarantar ’ya’yansu da shirya musu tarurruka don kwantar musu da hankali.

Daga nan sai shugabar ta yi kira ga mata cewa su ba su hadin kai da goyon baya don ba ’yan Darikar Tijjaniyya ne kadai suke cin gajiyar kungiyar ba. Kuma ta bukaci su shiga kungiyar a tafi tare, don ta haka ne za a gane matsalolin mata har a taimaka musu su fita daga cikin kuncin rayuwar da suka samu kansu ciki.

Taron ya samu halartar mata daga jihohin kasar nan da suka hada da daga Babban Birnin Tarayya Abuja da Borno da Kano da Bauchi da sauransu.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya