✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Matasan Arewa ta himmatu dan wayar da kan ‘yan kasuwa a Legas

Mataimakin Shugaban Kungiyar Matasan ’Yan kasuwa ’Yan Arewa mazauna Jihar Legas Malam Abubakar Usman Baso, ya shaida wa Aminiya cewa kungiyar tana gudanar da taron…

Mataimakin Shugaban Kungiyar Matasan ’Yan kasuwa ’Yan Arewa mazauna Jihar Legas Malam Abubakar Usman Baso, ya shaida wa Aminiya cewa kungiyar tana gudanar da taron kara wa juna sani a duk ranar Lahadi inda take hado mambobinta su tattauna muhimman abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya tare da bada dama a yi tambayoyi domin fidda jaki daga duma.

Ya ce suna yin haka ne ganin cewa Jihar Legas jiha ce da ke samun dimbin baki daga sassan kasar nan ciki har da Arewa inda akan samu tarin matasa da ke tururuwar zuwa Legas domin gudanar da harkokin  yau da kullum, sai da ’yan Arewa da dama kan samu kansu a halin tsaka-mai-wuya saboda rashin fahimta ko rashin sanin dokokin jihar. “Hakan ya sanya mu matasan Arewa ’yan kasuwa da ke harkokin kasuwanci a Kasuwar Kayan Gwari ta Mil 12 muka yi hubbasar wayar wa matasa ’yan uwanmu kai game da tsarin zaman Legas da kuma bin ka’ida da doka tare da kare martabar ’yan Arewa da ke zaune a jihar,” inji shi.

Ya ce “Jihar Legas jiha ce da ake bukatar mazauna cikinta su fahimci dokoki da ka’idojin da aka gindaya domin mutum ya kiyaye ya zauna lafiya. A Legas ce za ka ga an ce ba a yarda mutum ya tsallaka titi ta bangaren kaza ba, ba a ajiye mota a shiyya kaza ko ba a bin hanyar kaza. Sau tari al’ummarmu kan saba wadannan dokoki ba da gangan ba sai don rashin sani, wani ya shigo ba ya jin Yarbanci babu Turanci ka ga in irin haka ta kasance sai karamar magana ta zama babba.Don haka muka yi sauri muka kafa Kungiyar Ci gaban ’Yan kasuwar Arewa a Legas, mun yi wa wannan kungiya rajista kuma muna bin duk matakin da ya kamata don ganin ta cimma manufofin da aka kafa ta a kai.”

Ya ce, baya ga taron da suke yi duk ranar Lahadi suna gabatar da ayyuka na musamman na ci gaban al’umma da suka shafi taimakon kai-da-kai da aikin gayya da ziyarar wuraren da ’yan Arewa ke harkokinsu a Legas da jihohi makwabtanta, kuma suna shirya bitoci domin kara wa juna sani.

Sakataren Kungiyar Malam Auwal Na- Allah Kiru, ya shaida wa Aminiya cewa kungiyar na da manufofin da suka hada da hada kan al’ummar Arewa mazauna Legas da samar wa matasa sana’ar dogaro da kai da fahimtar da su dabarun zama jihar.  Ya ce koda yake akwai kungiyoyi da dama da a baya aka kafa su wasunsu ba sa kaiwa ko’ina sai a daina jin duriyarsu, amma su ana su bangaren sun yi shiri sosai kuma da yardar Allah za su kai ga gaci.

“Fatarmu ci gaban al’ummarmu tare da kyautata rayuwarsu, kuma alhamdulillahi muna samun goyon bayan jama’a domin suna da tabbacin kyawawan manufofin kungiyar domin a yanzu muna da akalla mambobin 700 a Legas kuma akwai ’yan uwanmu da ke jihohi makwabtanmu da su ma ke nuna sha’awar shiga a yi tafiyar da su. Mun kafa wannan kungiya ce domin ci gaban al’ummarmu da kare ta ta hanyar bin doka da oda,” inji shi.

A karshe shugabannin kungiyar sun nemi goyon bayan shugabannin al’ummar yankin da suka hada da sarakunan gargajiya da iyaye da jagororin ’yan kasuwa da al’ummar Arewa mazauna Legas.