Da Dumi Dumi

Kungiyar Matasan Kaura ta koka kan rashin wutar lantarki

Kungiyar Matasan Karamar Hukumar Kaura (Kaura Youth Coalition) da ke Jihar Kaduna, ta ziyarci kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KEDCO) da ke Kagoro a Karamar Hukumar, inda ta kai kokenta kan matsalolin da mutanen yankin ke fuskanta da suka hada da tsadar kudin wutar lantarki da rashin samun wutar tare da bukatar a samar musu da mita don lissafa iya abin da mutum ya yi amfani da shi ya biya.

Shugaban Kungiyar ta Kasa, Derek Christopher, wanda kuma ya jagoranci wadanda suka kai koken ya ce sun je ofishin ne don nuna damuwarsu kan matsalolin da suke addabarsu da bukatar kamfanin ya yi gyara kan yadda yake rabon wutar lantarkin.

“Duk da tsadar kudin da kuke yi na fitar hankali ba tare da wata shaida da ke nuna mutum ya sha wutar lantarkin ba, saboda babu mita da ke nuna haka, amma ba ma ganin wutar da ake sanya mu biya,” inji shi.

Yayin da yake maida jawabi, Manajan Riko na Kamfanin KEDCO da ke Kagoro, Mista Sabage Karl ya yaba wa kungiyar kan matakin da ta bi wajen bayyana damuwar jama’arta cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Ya ce duk da dai babu wani tsayayyen tsari kan rabon takardun biyan kudin wutar lantarki, amma sun daina amfani da tsohuwar mita ce don rashin bayyana hakikanin wutar da aka sha.

“Duk da haka idan mutum yana da wani korafi ko yana ganin ana tsuga masa kudin wuta, to ya kawo korafinsa a rubuce don kamfanin ya duba kuma za mu mika duk inda ya kamata mu kuma yi abin da ya kamata,” inji Manajan.

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya