✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Miyetti Allah ta goyi Gwamnatin Nasarawa kan hana barace-barace

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders ta Kasa reshen Jihar Nasarawa ta ce tana goyon bayan dokar hana bara a manyan titunan jihar da gwamnatin jihar…

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders ta Kasa reshen Jihar Nasarawa ta ce tana goyon bayan dokar hana bara a manyan titunan jihar da gwamnatin jihar ta kafa kwanan nan.

Shugaban Kungiyar ta Jihar, Alhaji Mohammed Husaini ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya, a Sakatariyar Kungiyar da ke Lafiya fadar jihar.

Ya ce kungiyar ba za ta ci gaba da zura ido tana kyale wadansu iyaye Fulani suna ci gaba da turo ’ya’yansu suna daukar nauyin kansu ta hanyar barace-barace da sunan karatu ba. Ya ce: “Shi ya sa ma tuni muka umarci mambobinmu su daina tura ’ya’yansu barace-barace kan kowane dalili. Kuma akwai hukunce-hukunce daban-daban da muka tsara ga duk mambanmu da ya karya dokar don ya kasance izina ga masu niyyar yin haka.”

Alhaji Mohammed Hussaini ya yaba wa Gwamman Jihar, Injiniya Abdullahi Sule, dangane da hangen nesan da ya yi na hana barace-barace a jihar; inda ya yi alkawarin bai wa gwamnatin cikakken goyon baya wajen tabbatar da nasarar dokar.

Ya ci gaba da cewa: “Ina kuma yin kira ga gwamnatin jihar nan a madadin al’ummar Fulani baki daya cewa ta yi wa Allah da Annabi (SAW) ta inganta harkokin karatun ’ya’yan makiyaya a jihar nan; musamman ta samar wa ’ya’yanmu karin ingantattun kayayyakin karatu da kwararrun malamai don cimma burin kafa makarantun da kuma kawar da su daga barace-barace a titunanmu. Kuma a namu bangare a matsayin kungiya za mu ci gaba da tallafa wa kokarin gwamnati ta hanyar gina karin ajujuwa da sauransu.”

Kuma ya bukaci gwamnatin jihar ta rika tunawa da mambobinsu a duk lokacin da take daukar ma’aikata da nade-naden siyasa da sauransu don karfafa su, su san amfanin neman ilimi. Ya ce gwamnatocin jihar a dukkan matakai ba sa yi da su a wadannan bangarori.

Sai ya bukaci al’ummar Fulani a jihar da kasa baki daya su dukufa wajen neman ilimin addini da na zamani domin dogara da kai tare da samun nasara a rayuwa.