Categories: KungiyoyiSana'o'i

Kungiyar MSS ta yi biki ban-kwana da shugabanninta

A ranar Lahadin da ta gabata ce Kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa reshen Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Rafin Raga da ke garin Kafanchan ta yi bikin ba-kwana ga shugabanninta da suka kammala shugabancin kungiyar bayan kammala karatunsu na babbar sakandare.

A lokacin da yake jawabi mai taken ‘Muhimmancin Ilimin Zamani,’ Malam Tasi’u Sulaiman,Talban Kachiya, ya ce ilimi kowane iri ne yana da muhimmanci a rayuwa inda ya jawo hankalin matasa su rungumi ilimin zamani kasancewa a halin da kasar ke ciki duk kokarin mutum matukar bai mallaki shaidar karatu na zamani mai zurfi ba, ba za a ci gajiyar kokarinsa yadda ya kamata ba. Ya hori daliban su rika neman shawarar masana kan kwasa-kwasan da za su zaba don fadada karatunsa a matakin gaba da sakandare.

ADVERTISEMENT

Malam Tasi’u, wanda tsohon Rajistara ne a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya, ya shawarci daliban su rungumi sana’a domin a cewarsa, hakan zai tallafa wa harkar neman iliminsu da sauran bukatun rayuwa.

Yayin gabatar da kasida ta biyu kan ‘Illolin Shaye-Shaye,’ Hajiya Zainab Kabir, wacce ma’aikaciyar kiwon lafiya ce, ta bayyana harkar maye da cewa ita ce amfani ko shan kwayoyin magani ko wasu sinadarai ba tare da iznin likita ko wani jami’in kiwon lafiya ba.

ADVERTISEMENT

Malama Zainab, ta ce illolin shaye-shaye a wannan zamani da maza da mata suka tsunduma a ciki na komawa ne zuwa ga al’umma gaba daya.

“Duk lokacin da kwakwalwarka ta fara sawwala maka wasu abubuwa da ba daidai ba, to ka je a bincike ka. Idan ba haka ba a karshe za ka ji an ce wane ya soki wane da wuka ko wance ta soki wance da wuka, inda illolin hakan ba a nan kawai ya tsaya ba, tunda yakan shafi kowace gaba da ke jikin mutum da suka hada da koda da hanta da huhu da kwakwalwa da kuma zuciya,” inji ta.

A karshe ta jawo hankalin matasa su nisanci cewa duk wani abu da hulda da shi zai jefa lafiyarsu da rayuwarsu cikin hadari wanda a karshe mutum zai kasance ba zai iya amfanar kansa da komai ba ballantana al’ummarsa.

. .

Recent Posts

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

1 min ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago