Da Dumi Dumi

Kungiyar NAGARTA ta wayar da kan matasa kan shaye-shaye

Kungiyar Wayar da kai tare da ci gaban matasa ta Nagarta Youth Debelopmet ta gudanar da taron wayar da kan matasan Jihar Kano a kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Tunda farko a jawabin maraba, Shugaban Kungiyar Kwamared  Aminu Idris ya ce  rashin ilimi ne babbar matsalar da ke haifar da shaye-shaye a fadin kasar nan.

Ya bayyana cewa idan gwamnati za ta ba su hadin kai za su iya kawar da harkar shaye-shaye a fadin Jihar Kano.

“Idan har gwamnati za ta ba mu dama insha Allah za mu iya kawar da harkar shaye-shaye a jihar nan,” inji shi.

A jawabin Shugaban Hukumar Shige da Fice ta kasa reshen Jihar Kano  Mustapha Muhammad Fagge ya ce baki ne ke shigowa da yawancin kayan shaye-shaye cikin Jihar Kano, don haka hukumarsu ta tashi tsaye wajen bullo da hanyoyin dakile shigowar baki cikin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Mustapha Fagge ya yi kira ga shugabannin gargajiya musamman masu unguwanni su sanya idanu a kan mutanen da ke unguwarsu musamman baki don gano abubuwan da suke gudanarwa tare da sanar da hukuma a kan lokaci.

A jawabin Malam Ibrahim Khalil ya bayyana cewa dole sai iyaye sun mike wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu sannan za a samu gyaruwar lamura a kasar nan.

“Iyaye su dage wajen tarbiyyar ’ya’yansu tare da yarda cewa makwabcinka zai iya hukunta danka ba tare da ka nuna bacin rai ba. To haka ne za a samu lamura su gyaru, domin ita tarbiyya ta kowa da kowa ce. Don haka sai kowa ya bayar da gudunmawarsa sannan za a kawo karshen shaye-shaye a tsakanin matasa da sauransu.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya