✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar OIC ta yi watsi da shirin zaman lafiya na Donald Trump

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi, (OIC) ta yi watsi da shirin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a kwanakin baya na tsarin wanzar da…

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi, (OIC) ta yi watsi da shirin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a kwanakin baya na tsarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar da ke wakiltar Musulmi biliyan daya da rabi a fadin duniya ta ki amincewa da shirin da bai wakilci dukkan bangarorin ba da kuma hakkin Falasdinawa.

Kungiyar mai mambobi 57 ta fara wani taron koli ranar Litinin a birnin Jeddah na kasar Saudiyya domin tattaunawa kan shirin na Trump,inda ta fadi a cikin wata sanarwa cewa “Tana kira ga dukkan mambobinta da kada su yadda su bayar da kai ga shirin ko kuma su bada hadin kai ga gwamnatin Amurka wajen aiwatar da shirin zaman lafiyar na gwamnatin Shugaba Trump.”

Kungiyar ta jaddada goyaon bayanta ga kasancewar Gabashin Birnin Kudus a matsayin Babban Birnin Falasdinawa.

Taron wanda shugabannin Falasdinawa suka nemi a gudanar da shi, ya zo ne kwana biyu bayan da Kungiyar Hada kan Kasashen Larabawa (Arab League) ta yi watsi da shirin a wani taron da ta yi a birnin Alkahira na Masar wanda aka yi wa lakabi da  “Yarjejeniyar Karni.” Tana mai cewa: “Bai kunshi mafi karancin hakkoki da kuma hankoron al’ummar Falasdinawa ba.”

Ta ce zaman lafiya zai inganta ne kawai idan Isra’ila ta janye daga kawanyar da ta yi wa yankunan Falasdinawa a yankin Gabas ta Tsakiya a 1967.