✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Musulmi ta yi watsi da shirin zaman lafiya na Donald Trump

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi, (OIC) ta yi watsi da shirin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, da ya ya gabatar a kwanakin baya na…

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi, (OIC) ta yi watsi da shirin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, da ya ya gabatar a kwanakin baya na tsarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar mai membobi 57 ta fara wani taron koli a yau Litinin a birnin Jeddah na kasar Saudi Arabia, domin tattaunawa kan shirin na Trump, ta fada cikin wata sanarwa mai cewa, “Tana kira ga dukkanin membobinta da ka da su yadda su bayar da kai ga shirin ko kuma ma su bada hadin kai ga gwamnatin Amurka wajen aiwatar da shirin zaman lafiyar na gwamnatin shugaba Trump.”

Taron wanda shugabannin Falasdinawa suka nemi da a gudanar da shi, na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Kungiyar Hada kan Kasashen Larabawa ta ‘Arab League ita ma ta yi watsi da shirin da aka yi wa lakabi da suna, “Yarjejeniyar Karni”, tana mai cewa: “Bai kunshi mafi karancin hakkoki da kuma hankoron al’ummar Falasdinawan ba.”