Search
Subscribe
Kungiyar PSN ta tallafa wa marasa lafiya 1,000 da magani

’Ya’yan Qungiyar PSN yayin tantancewar a Zariya

Kungiyar PSN ta tallafa wa marasa lafiya 1,000 da magani

Kungiyar Masu Harhada Magunguna ta Kasa (PSN) reshen Jihar Kaduna ta gudanar da rabon tallafin magunguna ga marasa lafiya 1,000 kyauta a garin Zariya. Da take bayanin makasudin shirin bayar da magunguna ga marasa galihu wanda ya gudana a fadar Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, Shugabar Kungiyar Hajiya A’isha Isyaku Tukur, ta ce yana daga cikin shirye- shiryen na karbar bakuncin taron kungiyar na kasa da za a yi a Kaduna.

Hajiya A’isha Isyaku Tukur, ta ce taron da za su karbi bakunci shi ne karo na 92 wanda a  bara garin Ibadan ya karbi bakuncinsa. “Saboda neman albarka daga uban kasa Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya sanya muka kawo tallafin magunguna da tantace marasa lafiya da kuma raba magungunan ga marasa galihu kyauta da muka  gudanar a fadar Mai martaba Sarkin Zazzau,” inji ta.

Shugaban Kungiyar ta ce magungunan da suka raba akwai na zazzabi da na hawan jini da ciwon suga da na tsutsar ciki da sauransu kuma suna sa ran tantace marasa lafiya kimanin dubu daya tare da ba su magungunan kyauta.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin