✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar PSN za ta dakatar da bayar da lasisin sayar da magani

Kungiyar Kwararru Masu Harhada Magunguna ta Kasa reshen Jihar Kano (PSN) ta bayyana takaicinta kan yadda yawan hada-hadar gurbatattun magunguna da kwayoyin ke karuwa a…

Kungiyar Kwararru Masu Harhada Magunguna ta Kasa reshen Jihar Kano (PSN) ta bayyana takaicinta kan yadda yawan hada-hadar gurbatattun magunguna da kwayoyin ke karuwa a tsakanin al’ummar jihar.

Shugaban Kungiyar PSN ta Jihar Kano, Bala Maikudi ya  ce daga yanzu kungiyar ta dauki matakin daina bayar da lasisin sayar da magani a kananan hukumomi takwas na kwaryar birnin Kano, saboda yawancin masu harkar sayar da maganin ba su da ilimin magani.

“Mun fahimci cewa wadannan kananan masu sayar da magunguna da aka fi sani da kyamis suna harkar magani ba tare da ilimin magani ba. Wanda ba ya da ilimin magani kuwa zai iya sayar da shi ba bisa ka’ida ba. To magani ba gyada ba ne da za a ce kowa zai sayar. Don haka dole ya zama an tsabtace harkar sayar da magani,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Muna daga cikin kwamitin da ke yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi don haka ba za mu nade hannu mu bari ana ci gaba da baza gurbatattu da miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma da sunan sayar da magani ba.”

Shugaban Kungiyar PSN din ya kara da cewa tun farko ana bude kananan wuraren sayar da  magunguna ne ga al’ummar da ba su da damar samun manyan wuraren sayar da magunguna. “Ana bayar da izinin bude kananan wuraren sayar da magunguna ne a wuraren da ba su da manyan wuraren sayar da magani, kuma a cikin kwaryar Kano muna da su da yawa, don haka ba a bukatarsu,” inji shi.

Bala Maikudi ya yi kira ga jama’a su rika sanar da hukuma game da wani abu da ba su yarda da shi ba na sayar da magani marar kyau ko kuma na shaye-shaye masu kawar da hankali. “Ba  za ka iya yin abu idan ba ka san da shi ba, al’umma su ne idanuwanmu. A duk lokacin da jama’a suka ga wani yana sayar da jabun magani ko miyagun kwayoyoi da kayan maye, ko kuma aka samu wani yana sarrafa su, to su yi gaggawar sanar da mu, domin mu kuma za mu dauki matakin da ya dace za mu iya zuwa mu kwace su,” inji su.