✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Shi’a ta yi wa mata bitar zamantakewar aure da sana’a don dogaro da kai

Kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a mabiyan Shaikh Ibrahim Zakzaki ta shirya wa matan aure taron bitar zamantakewar aure tare da nusar dasu mahimmanci…

Kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a mabiyan Shaikh Ibrahim Zakzaki ta shirya wa matan aure taron bitar zamantakewar aure tare da nusar dasu mahimmanci sana’ar dogaro da kai bangaren mata na kungiyar ne ya shirya taron bitar na kwanaki uku a birnin Legas inda aka gabatarwa matan jawabai tare da koyar da su sana’oin hannu domin dogaro da kai.   Malama Khadija Mustapha Malumfashi ita ce, ta jagoranci gabatar da bitar ta shaidawa Aminiya cewa, rashin hakuri shi ne musababbin mafi yawan matsalolin da akan samu a al’almuran da suka danganci aure lamuran da a yanzu suka kai ga yin muni har akan kai ga yin kisa ko mummunan rauni, “Haquri tushe ne a zamantakewar aure kana tun ran gini tun ran zane dole ne a dinga yin cikakken bincike kafin a kai ga aure domin samun zamantakewar aure mai cike da fahimtar juna da walwala. “Tace wajibi ne matan aure su koyi sana’ar dogaro da kai domin rage radadin talauci tare da taimakon juna, “Don haka muka yi masu bitocin sana’oin dogaro da kai mun kuma koya masu sana’o’in da suka hadar da yin sabulu, man shafawa da dai makamantan su, idan mace tana da sana’a zata sami karin kima da daraja”. In ji ta. 

A karshen bitar da suka gabatar ‘yan kungiyar sun yi gangami na lumana inda suka nemi gwamnatin shugaba Buhari ta saki shugaban su Sheikh Ibrahim Alzakzaki wanda suka ce yana bukatar kulawar likitoci, suka ce likitoci sun tabbatar masu da cewa, akwai guba a jikinsa wanda ya samu a sakamakon harbin da jami’an tsaro suka yi masa don haka suke kiran a sako shi domin a bashi damar kulawa da lafiyarsa.