✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar TAN ta bukaci Lalong ya bunkasa wuraren bude-ido

Kungiyar Masu Yawon Bude-Ido ta Najeriya reshen Jihar Filato (TAN) ta shawarci gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta wuraren shakatawa da yawon bude-ido…

Kungiyar Masu Yawon Bude-Ido ta Najeriya reshen Jihar Filato (TAN) ta shawarci gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta wuraren shakatawa da yawon bude-ido ta hanyar zuba jari a fannin, domin samun kudin shiga, musamman ma a yanzu da farashin man fetur ke kara faduwa a kasuwar duniya.

Shugaban kungiyar Mista Dung Anthony ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida a Jos a ranar Litinin.
Mista Dung ya ce Gwamnatin Jihar Filato ta mayar da hankali kan wadannan wurare don samun kudin shigar da za su sa jihar ta rage dogara da abin da take samu daga Gwamnatin Tarayya.
Ya ce idan gwamnati ta zuba jari a wadannan wurare, jama’a za su rika dafifin zuwa jihar don yawon bude da kuma shakatawa, musamman ma da yake jihar tana da abubuwan tarihi da al’adu da na nishadantarwa masu kayatarwa, kuma tana da yanayi mai kyau.
“Idan kuka lura Jihar Filato tana da abubuwan al’adu da tarihi kamar Dutsen Riyom da na Shere da koramar Assop da Dutsen Wase da Gidan Tarihi na MOTNA da koramar Kurra da Dutse Mai Aman Wuta da ke Kurang da fadamar kamun kifi ta Panyam da gidajen namun daji da tafkin Pandam da sauransu.  Don haka akwai bukatar Gwamnatin Jihar a karkashin Gwamna Simon Bako Lalong ta zuba jari a wadannan wurare, domin yin hakan zai samar da ayyukan yi, kuma zai rage radadin talauci, zai kuma samar wa jihar karin kudin shiga, musamman ma a yanzu da farashin man fetur yake kara faduwa,”  inji shi.