✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Tunawa da Sardauna ta karrama Sadik Plaza

Kungiyar Dalibai, ta tunawa da marigayi tsohon Firayi Ministan Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Reshen Jami’ar Jos ta karrama fitaccen mai taimaka wa…

Kungiyar Dalibai, ta tunawa da marigayi tsohon Firayi Ministan Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Reshen Jami’ar Jos ta karrama fitaccen mai taimaka wa al’ummar nan da ke Jos, Alhaji Abubakar Sadik Plaza, kan ayyukan taimakon jama’a da yake yi a garin Jos  da kewaye a ranar Juma’ar da ta gabata.

Da yake jawabi lokacin da yake mika wa Alhaji Abubakar Sadik shaidar karramawar, Shugaban Kungiyar Tunawa da Sardauna, Malam Haruna Yusuf Abba ya ce, ganin irin ayyukan taimakon jama’a da Alhaji Sadik Plaza yake yi, ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, ya sanya suka karrama shi. Domin ya yi daidai da yadda marigayi Sarduna ya yi, lokacin da yake raye.

Ya ce yanzu  babu inda ayyukan taimakon jama’a da Alhaji Sadik Plaza yake gudanarwa bai shiga  ba, a cikin garin Jos da kewaye.

Ya ce kadan daga cikin ayyukan taimakon jama’a da ya yi, sun hada da samar da famfunan tuka-tuka a Unguwar Rogo da  gina gada a ’Yan Daddawa da gina  gada a cikin Kabong.

Har ila yau ya ce akwai asibitoci da dama da ya  gyara a cikin garin Jos, kuma yanzu yana nan yana gina wani asibiti, a Garba Daho a garin Jos.

Haka zalika ya ce ya yi  famfunan tuka-tuka a wurare da dama a Karamar Hukumar  Jos ta Gabas, baya ga daruruwan mutane da yake tallafawa wajen biyan kudaden magani a asibitoci da makarantu.

“Don haka  muka  karrama shi tare da ba shi  sarautar Makama Babba, don karfafa masa gwiwa kan wadannan ayyuka, na taimaka  wa al’umma da ya sanya a gaba,” inji shi.

Da yake mayar da jawabi, Alhaji Abubakar Sadik Plaza ya bayyana matukar farin cikinsa, da wannan karramawa da aka yi masa.

Ya ce babban  abin da ya karfafa masa gwiwa a ayyukan tallafa wa jama’a, shi ne addinanmu na Musulunci da Kirista sun nuna muhimmancin taimaka wa jama’a.

“A kullum idan na ga wani abu da jama’a suke bukata a shirye nake in taimaka musu, ko a bangaren Musulmi ko a bangaren Kirista. Kuma ina yin wadannan abubuwa ne saboda Allah da kuma fatar ’yan baya su gani su yi koyi,’’ inji shi.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar Jihar Filato  su ci gaba da zaman lafiya, domin a samu ci gaba a jihar.