Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar yakin neman zaben Buhari ta nemi hadin kan sauran kungiyoyi

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaba Muhammadu Buhari (BCO), Sarkin Kudun Yamma, Alhaji Hassan Isyaku, ya yi kira ga sauran kungiyoyi masu fafutuka irin wannan, su janye jiki daga yin siyasar da ba za ta amfani Najeriya ba.

Ya ce, “lokacin da muke ciki a yanzu da babban zaben kasa ke karato wa, lokaci ne da zamu kara zage damtse wajen tunkarar abokan hamayya amma ba lokaci ne na kace-nace a tsakaninmu ba.”

ADVERTISEMENT

Alhaji Hassan Isyaku ya fadi haka ne a yayin da yake zantawa wa da manema labarai a Ibadan a lokacin da yake kare kungiyarsu ta (BCO) da wasu ke zargin ta aika da wasikar neman alfarmar kwangila ga Ministan Ayyuka da Gidaje da Wutar Lantarki, Babatunde Fashola.

Ya ce, “babu kamshin gaskiya a kan wannan zargi, domin tun tuni muka sadaukar da kanmu wajen kafa wannan kungiya da muka fara da kafa sashen Kudu maso Yammacin Kasar nan kafin ta hada kasa baki daya. Saboda haka babu abun da zai tsokane mana ido da zai kaimu ga mika kokon bara ga ministoci. Tun da muka fara bamu taba zuwa neman wata alfarma daga Gwamnoni ko Ministoci ba, muna yin aikin ne daga cikin aljihunmu.”

ADVERTISEMENT

“Ya kamata mu daina yi wa juna kazafi da bakaken maganganu. Nauyin da muka dora wa kawunanmu shi ne ya kamata mu fuskanta domin hakan ne zai sa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu karbuwa daga hannun miliyoyin jama’ar kasa da suka sa ido su ga irin tafiyar da muke yi. Muddin muka cusa wani abu a cikin zukatanmu fiye da wannan manufa, to kuwa zamu dandana kudarmu,” inji shi.

Sarkin Kudun na Yamma wanda yana daga cikin Dattijai na Kungiyar ta (BCO) ya yi kira ga Daraktan Yakin neman Zaben Buhari a shekara ta 2019 Mista Rotimi Amaechi kada ya saurari baragurbin mambobi da ake amfani da su domin wargaza al’amura. Ya ce, “ya kamata ka janyo sanannun mutane masu kyawawan halaye da za ku gudanar da wannan aiki tare tsakani da Allah, kada ku janyo mutane masu hankoron kawunansu ba ci gaban kasa ba.”

Da yake amsa wata tambaya, Hassan Isyaku cewa ya yi “yanzu haka mun kammala aikin bude manyan ofisoshin yakin neman zaben Buhari a jihohin Kudu maso Yamma da wasu jihohi na Arewacin kasar nan kuma dukkan al’ummar Hausa da Fulani dake zaune a wannan sashen sun nuna gamsuwarsu da irin bayanan da ofisoshin suke dauke da su. Yanzu haka muna nan mun fara shiga cikin kauyuka da dazuka domin wayar da kan jama’armu a kan shirin babban zabe mai zuwa.”